Karamar Sallah: Ibrahim Babangida da ‘Ya ‘ya da Jikoki su na bikin idi
- Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi hutun sallar bana tare da Iyalinsa
- Tsohon Shugaban Najeriyar ya dauki hoton sallah tare da ‘ya‘ya da jikokinsa
- Dele Momodu ne ya fito da wannan hoto a shafinsa na sadarwa na Instagram
Fitaccen tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi bikin karamar sallar wannan shekara ta 1441 a cikin iyalinsa a cikin farin ciki.
Tsohon shugaban kasar sojin ya dauki hoto da ‘ya ‘yan sa da kuma jikoki duk ana dauke da farin ciki. An yi wannan hoto ne Babangida ya na zaune a kan kujera.
Shararren ‘dan jaridar nan, Cif Dele Momodu ne ya fara wallafa wannan hoto a kan shafinsa na Instagram a jiya watau ranar Talata, 25 ga watan Mayu, 2020.
Mutane kusan 5, 000 su ka nuna sun yi sha’awar hoto, da-dama kuma sun yi wa tsohon shugaban kasar na su addu’a, su na yabon abin alherin da ya yi a mulki.
Za a ga maza biyu da mata biyu tare da Janar Ibrahim Babangida mai ritaya. Daga ciki har da wani matashi cikin babbar riga wanda ya ke kama da Mahaifinsa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari da Iyalinsa sun yi sallar idi a fadar Shugaban kasa
Haka zalika za a ga Babangida ya rike wani jikinsa a cinya a lokacin da ake hoton. A ranar Lahadi ne mafi yawan musulman Duniya su ka yi bikin karamar sallah.
Ibrahim Badamasi Babangida mai shekaru 78 ya yi mulkin Najeriya daga 1985 zuwa 1993. Yanzu shekaru kusan 27 ake nema da IBB ya bar kan karagar mulkin kasar.
Daga cikin ‘ya ‘yan tsohon shugaban da mu ka sani akwai Aisha, Muhammad, Aminu da kuma Halima Babangida, wasu daga cikinsu ne su ka haifa masa jikokinsa.
A 2009, mai dakin shugaban, Maryam Babangida ta rasu bayan sun shafe shekaru 40 su na zaman aure. Babangida ya nuna bai da niyyar kara aure a daidai wannan lokaci.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng