Karamar Sallah: Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya yi sallar idi a Legas
- A Ranar Lahadi Muhammadu Sanusi II ya yi sallar idi a gidansa da ke Legas
- Wannan ne karon farko da tsohon Sarkin zai yi sallah bayan barin gidan dabo
- Mutane sun rika kawowa Mai martaban gaisuwar sallah a safiyar Yau Lahadi
A yau 24 ga watan Mayu, 2020, mu ka samu labarin cewa mai martaba tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya gudanar da sallar idi a gidansa da ke Legas.
A yau Lahadi watau 1 ga watan Shawwal, 1441, mafi yawan musulmai a Najeriya da wasu kasashen Duniya su ke murnar karamar sallah bayan an sha ruwan azumi.
Ba a bar tsohon sarki Muhammadu Sanusi II wajen bikin sallar ba, mun samu labari daga Tuwita cewa Mai martaban ya rangado ado kamar yadda ya saba, ya bada sallar idi.
Wani bidiyo da mu ka samu dazu nan daga shafin @MSII_Dynasty ya nuna Malam Muhammadu Sanusi II yayin da ya fito daga dakinsa zai jagoranci sallar idi a safiyar yau.
KU KARANTA: Sarakunan Kano da Bichi sun ziyarci tsohon Ciroma, Sanusi Ado Bayero
Jama’a da-dama sun je gaban tsohon sarkin inda su ka durkusa, su ka gaida shi kamar yadda bidiyon ya nuna, an kuma ga fadawa cikin zauren na Muhammadu Sanusi II.
Mai martaban ya yi rawani mai kunne biyu inda kuma ya ke sanye da wata farar babbar riga da alfarma mai ratsin aiki launin ruwan gwal da ‘yar ciki da wasu tare da shi.
Mutanen da ke zagaye da tsohon sarkin su na ta ambaton Allah kamar yadda aka san Musulmai a ranar yau. Mai martaban ne ya ke jagorantar zikirin, su kuma su na biye.
Daga cikin wadanda su ka kai wa mai martaban gaisuwar har da wasu yara biyu da wata jaririya da aka tallaba aka kai ta gaban tsohon sarkin da aka cirewa rawani a Maris.
Wannan ne karon farko da Sanusi II zai yi idi a gida bayan sauke sa daga gadon sarauta. Idan ba ku manta ba kwanaki mai dakin Muhammadu Sanusi II ta haifi ‘diya mace.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng