Abin Bakin Ciki: Matashi Ya Kashe Abokinsa da Suke Aiki Wuri 1 kan Gardamar Siyasa

Abin Bakin Ciki: Matashi Ya Kashe Abokinsa da Suke Aiki Wuri 1 kan Gardamar Siyasa

  • An kashe wani matashi, Ibrahim Jadda, yayin d wata gardamar siyasa ta hada shi da abokinsa a wurin aikinsu a birnin Bauchi
  • Rahotanni sun ce saɓanin ya samo asali ne daga wata mahawarar siyasa da suka yi kwana guda kafin faruwar lamarin
  • ’Yan sanda sun kama Sallau a Liman Katagum da ke ƙaramar hukumar Bauchi, inda yake tsare a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Wani mutum mai matsakaicin shekaru, Ibrahim Jadda, ya rasa ransa, inda ake zargin abokinsa mai suna Sallau da kashe shi sakamakon wata gardama da ta ɓarke a wurin aikinsu da ke cikin birnin Bauchi.

Abokan biyu suna aiki tare ne a wani wurin wanke motoci mai yawan jama’a da ke kan titin Gombe a birnin Bauchi. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yadda 'yunwa' za ta ruguza lissafin Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027

Bauchi.
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta bayyana wa Tribune Nigeria cewa mutanen biyu sun yi wata mahawara mai zafi kan siyasa a ranar da ta gabata, kafin su tashi daga aiki.

A cewar majiyar, abokan aikinsu sun shiga tsakani tare da raba su domin hana saɓanin ya rikide zuwa faɗa da hannu.

Majiyar ta ƙara da cewa mutanen biyu sun rabu ba tare da sun gudanar da aikin da suka saba yi na ƙididdige kayan da suka rage da kuma raba ribar ranar ba. Wannan mataki ya fusata Sallau, kamar yadda aka bayyana.

Yadda aka gano Ibrahim

A ranar Alhamis, marigayi Ibrahim Jadda ne ya fara isa wurin aikin. Ya shiga wani ƙaramin ɗaki da ke cikin garejin domin sauya tufafinsa da kuma shirya fara aikin ranar.

A lokacin, akwai mota da tabarma da suke jiran a wanke. Bayan wasu ’yan mintuna, Sallau ya isa wurin, sannan ya shiga ɗakin inda ya tarar da Ibrahim yana shirin fara aiki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan bindiga sun rutsa shugaban matasan APC da matarsa a cikin gida

An ce Ibrahim ya gaishe da Sallau, amma bai amsa gaisuwar ba, da alama har yanzu yana riƙe da fushin saɓanin da suka yi a ranar da ta gabata.

Rahotanni sun yi zargin cewa Sallau ya zaro wuƙa mai kaifi, sannan ya soki Ibrahim a ƙirji, lamarin da ya sa jini ya riƙa zuba sosai.

Wata majiya kuma, wadda ke aiki a wani wurin wanke motoci da ke kusa, ta ce bayan Sallau ya soki Ibrahim, ya kulle ƙofar ɗakin sannan ya gudu ba tare da wani ya fahimci abin da ya faru ba.

An tarar da shi cikin jini

Majiyar ta bayyana cewa bayan wani lokaci, mutane suka fara tambayar dalilin da ya sa ba a bude wurin wanke motocin ba, duk da cewa akwai aikin da ake jira, kuma ba a ga Ibrahim ko Sallau ba.

Hakan ya tayar musu da hankali, inda wani ya je ɗakin domin duba abin da ke faruwa, amma ya tarar a kulle yake.

Ta ce wasu mutanen da ke kusa sun tabbatar da cewa sun ga mutanen biyu lokacin da suka isa wurin, amma ba su san abin da ya faru tsakaninsu ba.

Kara karanta wannan

Tinubu zai fara karɓar harajin 25% daga kuɗaɗen shigan ƴan Najeriya?

Daga bisani, aka ɓalla ƙofar ɗakin, inda aka tarar da Ibrahim kwance cikin jini, kuma yana dab da mutuwa.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yan sanda sun kama Sallau

Bayan an sanar da ’yan sanda, an garzaya da Ibrahim zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) domin samun kulawar likitoci. Sai dai, duk da ƙoƙarin da aka yi, likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.

Majiyar ta ƙara da cewa Sallau ya tsere daga wurin bayan faruwar lamarin, amma daga baya ’yan sanda suka gano inda yake a Liman Katagum, da ke cikin ƙaramar hukumar Bauchi, inda suka kama shi.

Kotu ta daure wanda ya kashe abokinsa

Kun ji cewa Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Ayuba Sani Tumfafi hukuncin daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali bayan ta same shi da laifin kashe abokinsa, Ibrahim Dan Larai.

Hukuncin ya biyo bayan wani saɓani da ya ɓarke tsakanin Ayuba da marigayin kan tashi domin yin sallar Asuba, wanda daga baya ya kai ga mutuwar Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262