Sarkin Musulmi ya yi bayani game da yadda ake Sallar Idin mutum 1 a gida

Sarkin Musulmi ya yi bayani game da yadda ake Sallar Idin mutum 1 a gida

Kungiyar Jama’til Nasril Islam, JNI, dake karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi ta yi bayani game da sabon salon sallar Idi da za’a yi a karamar sallar bana.

Idan za’a tuna, a sanadiyyar yaduwar annobar COVID-19, jahohi da dama basu sassauta dokar zaman gida ba, wanda hakan ke nufin jama’a zasu yi sallar Idi a kulle a gidajensu kenan.

KU KARANTA: Dandazon masu bin gwamnati bashin kudi sun hana Sabo Nanono shiga ofis a Abuja

Daga cikin jahohin akwai Kaduna, Abuja da wasu jahohin kudancin Najeriya, don haka NSCIA ta fitar da sanarwa inda take shaida ma Musulmai yadda zasu gudanar da sallar Idi a gida.

Daily Trust ta ruwaito babban sakataren JNI, Sheikh Khalid Abubakar ne ya fitar da sanarwar a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu, inda ya jaddada sakon Sarkin Musulmi na a yi sallah a gida.

Sarkin Musulmi ya yi bayani game da yadda ake sallar Idin mutum 1 a gida
Sarkin Musulmi a Idi Hoto: The Defender
Source: UGC

“Sallar Idi nafila ce mai raka biyu,

“A raka’ar farko ana kabbara guda 7

“Sai a karanta Suratul Fatiha

“Sai a karanta abin da ya sawwaka daga Al-Qur’ani, musamman suratul A’ala

“A raka'a na biyu kuma kabbara 5 ake yi

“Sai a karanta Suratul Fatiha

“Sai a karanta abin da ya sawwaka daga Al-Qur’ani, musamman suratul Ghashiyah.

“Amma tun da sallar gida ne, ba lallai sai an yi hudubar bayan Sallah ba.

“Duka wadannan sun tabbata a hadisin Anas bin Malik dake cikin Sahihul Bukhari, da mazhabar Malikiyya, a Mukhtasar ma Al-Kharshi da Al-Munah Al-Jalil sun yi bayaninsa.” Inji shi.

Ya ce a jahohin da gwamnatoci suka amince a gudanar da Idi, an shawarci jama’a su dabbaka dokokin da aka shimfida na kare yaduwar cutar wanda masana kiwon lafiya suka yi umarni.

Malamin ya ce jama'a su sanya takunkumin fuska, su wanke hannuwansu da sanitizer, kuma su bada tazara a tsakaninu, ba kuma lallai bane a tafi filin Idi, ana iya yi a Masallatan unguwanni.

“Malamai su ji tsoron Allah su nuna dattaku wajen furucinsu da kuma ayyukansu don kare mutuncin addinin Musulunci da al’ummar Musulmai gaba daya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel