Tsohon Shugaban Amurka Ya Jawo Ayar Kur'ani, Ya Soki Cin Mutuncin Musulmao
- Bill Clinton ya ce ya gaji da yadda wasu ke cin zarafin Musulmi saboda addininsu, yana mai kira da a kawo ƙarshen nuna ƙyama
- Tsohon shugaban na Amurka ya tuna yadda ’yarsa, Chelsea Clinton, ta gabatar da shi ga Alƙur’ani tun tana yarinya, inda ya jaddada muhimmancin fahimtar juna tsakanin al’ummomi
- Jawabinsa ya zo ne a daidai lokacin da ɗan takarar Majalisar Dattawan Amurka, Abdul El-Sayed, ke fuskantar suka kan addininsa yayin neman kujerar Michigan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Florida, Amurka - Tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton, ya yi Allah-wadai da kalaman nuna ƙyama ga Musulmai da wariyar addini.
Bill Clinton ya bayyana cewa ya gaji da yadda wasu ke kai wa Musulmai hari saboda kasancewarsu Musulmai.

Source: Getty Images
Bill Clinton ya yi magana kan Musulmai
Clinton ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a cocin Koinonia Worship Center da ke jihar Florida, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.
Ya yi amfani da wani saƙo daga Alƙur’ani wajen jaddada muhimmancin fahimtar juna tsakanin mutanen da suka fito daga al’adu da addinai daban-daban.
“Na gaji da yadda mutane ke wulaƙanta Musulmai saboda kawai su Musulmai ne,” in ji shi.
Tsohon shugaban kasar ya soki rashin haƙuri tsakanin mabiya addinai da kuma abin da ya bayyana a matsayin ƙarin rarrabuwar kawuna ta fuskar addini da al’adu a Amurka.
Yadda ’yarsa ta gabatar da shi ga Alƙur’ani
Clinton ya bayyana cewa ’yarsa, Chelsea Clinton, ce ta fara gabatar da shi ga Alƙur’ani lokacin da take matashiya.
A cewarsa, Chelsea ta karanta littafin mai tsarki na Musulunci, daga bisani ta ƙarfafa shi da ya karanta shi domin ya fahimci saƙonnin da ke cikinsa.
Tsohon shugaban ya ce saƙon da ya karanta yana nuna cewa ya kamata mutane daga al’ummomi daban-daban su yi ƙoƙarin fahimtar juna, maimakon mayar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu sanadin ƙiyayya da rikici.
Wannan saƙo ya yi daidai da aya ta 13 a cikin Suratul Hujurat, inda Alƙur’ani ya bayyana cewa Allah ya halicci mutane daga al’ummai da ƙabilu daban-daban ne domin su san juna.
Bill Clinton ya yi nasiha
Clinton ya jaddada cewa bai kamata mutane su yi amfani da bambancin addini a matsayin hujjar nuna wariya ko ƙiyayya ga wasu ba.
Ya kuma bayyana cewa akwai mutanen da ke aikata ba daidai ba a cikin kowane addini, saboda ɗan Adam ba cikakke ba ne.
Saboda haka, ya buƙaci jama’a su ɗauki bambancin addinai da al’adu a matsayin wata dama ta ƙara fahimtar juna, maimakon ganin hakan a matsayin tushen rikici.

Source: Getty Images
Abdul El-Sayed na fuskantar suka kan addininsa
Jaridar Daily Trust ta ce jawabin Clinton ya zo ne a lokacin da ake ƙara samun muhawara a Amurka kan Musulunci da wakilcin Musulmi a harkokin siyasar ƙasar.
Wannan batu ya sake daukar hankali yayin da Abdul El-Sayed, ɗan takarar jam’iyyar Democrat, ke neman kujerar Majalisar Dattawan Amurka mai wakiltar jihar Michigan, inda yake fuskantar suka daga wasu abokan hamayyarsa kan addininsa.
El-Sayed, wanda ya taɓa riƙe muƙami a fannin kula da lafiyar jama’a, na neman zama Musulmi na farko da aka zaɓa zuwa Majalisar Dattawan Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa wasu abokan hamayyarsa na ƙoƙarin danganta shi da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi, duk da cewa ya fito fili ya yi Allah-wadai da ƙungiyar Muslim Brotherhood.
Shirin Amurka da Israila kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Amurka da Isra’ila sun tsara wasu takamaiman tsare-tsaren sake kai hare-hare kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka.
Wasu jami’an Amurka da wasu mutanen da aka sanar da su bayanan tattaunawar shirye-shiryen sojoji suka bayyana hakan.
Asali: Legit.ng


