Shugaban Faransa Ya Soke Ziyarar da Ya Shirya Kawowa Najeriya
- Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Najeriya a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026
- Ana danganta matakin da damuwa kan zanga-zangar da ake yi a Faransa, zaɓen shugaban ƙasar Najeriya mai zuwa da kuma cutar Ebola
- Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta samu wata sanarwa a hukumance kan soke ziyarar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Najeriya, sai dai rahotanni sun nuna cewa har yanzu ana iya samun sauyin matsaya.
Macron ya soke ziyarar tasa, wadda aka tsara gudanarwa a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, saboda damuwa kan zanga-zangar da ake ci gaba da yi a Faransa.

Source: Getty Images
Dalilan soke ziyarar Macron
The Cable ta rahoto cewa bayan zanga-zanga, ana ganin Macron ya soke ziyarar sabod zaɓen shugaban ƙasar Najeriya mai zuwa da kuma bullar cutar Ebola.
Majiyoyin Najeriya da aka yi wa bayani game da shirin ziyarar sun bayyana cewa Macron da Shugaba Bola Tinubu sun amince a ranar Alhamis da soke ziyarar aiki ta shugaban ƙasa.
Macron ya nuna fargabar cewa zuwa Najeriya a daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Faransa na iya zama kamar rashin damuwa da halin da ƙasarsa ke ciki, tare da nuna rashin ɗaukar alhaki.
Zanga-zangar tashin hankali da ta fara a ƙasar a watan Satumba ta jawo rufe makarantu sama da 900, sace-sacen kayayyaki da kuma arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro.
Matsalar da Tinubu ya hango
Rahotanni sun kuma nuna cewa Tinubu ya bayyana damuwa kan yiwuwar ziyarar Macron, wadda za ta gudana kusan watanni uku kafin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta jawo zargin katsalandan daga ƙasashen waje.
Tinubu dai na neman tazarce kan mulkin ƙasar duk da wasu ’yan ƙasa n nuna fushi kan yadda yake gudanar da mulki. .
Mutane da dama ba su gamsu da ayyukan gwamnatinsa ba, musamman dangane da tsadar rayuwa, hauhawar farashi, ƙarin kuɗin man fetur, rashin aikin yi da rashin tsaro.
Dangantakar Tinubu da Faransa
Dangantakar Tinubu da Faransa ma ta fuskanci suka daga jama’a. Ziyarar da Tinubu ya kai Paris a baya-bayan nan ta jawo suka, sakamakon rashin halartarsa a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 (UNGA) da kuma tsawaita hutun aikinsa.
Haka kuma, an nuna damuwa kan bullar cutar Ebola da aka tabbatar kwanan nan a Najeriya.
Premium Times ta tuntubi sashen yaɗa labarai na Ofishin Jakadancin Faransa kan soke ziyarar Macron, amma ofishin ya ƙi yin tsokaci.
An kuma tuntubi mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Olufemi Adeniyi, wanda ya ce ma’aikatar ba ta samu wani bayani kan soke ziyarar Macron ba.
“Ba mu da wannan bayani a halin yanzu. Idan aka samu sanarwa a hukumance game da lamarin, za mu fitar da ita,” in ji shi.
Asali: Legit.ng

