Bukukuwan Sallah: Abubuwa 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Yi Kafin Sallar Idi

Bukukuwan Sallah: Abubuwa 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Yi Kafin Sallar Idi

Tsokacin Edita: Azumin watan Ramadana ya zo karshe, domin kuwa a yau Laraba 12 ga watan Mayu ne ake azumtar rana ta 30 na watan. Gobe Alhamis, 13 ga watan Mayu zai zama daidai da 1 ga watan Shawwal wato, watan karamar sallah a Najeriya.

Dukkan musulmi na farin ciki da rana irin wannan, saboda haka ne ma ake ta shirye-shiryen bukuwan sallah, kama daga dinkin sabbin kaya har zuwa yanka dabbobi don rabarwa ga 'yan uwa da abokan arziki.

Akwai wasu abubuwa da ya kamata musulmi ya sani game da sallar Idi. Kasancewar Idi ibada, akwai wasu abubuwan da ya kamata a gudanar dasu ko dai kafin ranar Idi ko kuma a ranar Idi. Wani malami da aka tattauna dashi ya kawo wasu abubuwa 9 da ya kamata musulmi ya yi.

KU KARANTA: Yajin Aiki: Gwamnatin Ta Amince da Daya Daga Cikin Bukatun Likitocin Najeriya

BBC Hausa ta tattauna da Malam Nura Khalid limamin masallacin Apo a birnin tarayyar Najeriya Abuja wanda ya bayyana wasu abubuwa da ake son musulmi ya yi a ranar Sallar Idi kamar haka:

1. Bayar da zakkar fidda-kai ga mabukata

Zakatur fitr wajiba ce kamar yadda Annabi SAW ya farlanta ta. Ta fi falala a fitar da ita kafin a tafi masallacin Idi.

Amma an sawwaka a fitar da ita a daren Idi ko kwana biyu ko uku kafin ranar Idi, wato tun a ranar 27 na watan Ramadana musamman ga kungiyoyi ko wakilai da ke tattara zakka domin raba wa mabukata.

Fitarwa da wuri zai taimaka zakkar ta isa ga mabukata da wuri kafin lokacinta ya wuce.

2. Wankan zuwa Idi

Wankan zuwan Idi Sunnah ne. Ana son mutum ya yi wanka a ranar Idi kamar yadda yake wankan zuwa Juma'a.

3. Cin abinci kafin tafiya masallaci

Ana son mutum ya ci abinci kafin tafiya sallar Idi. Ba a so mutum ya jinkirta cin abinci domin ka da ya nuna kamar ana azumi, domin rana ce da ba a yin azumi.

Malamin ya ce Annabi SAW yana cin dabino kamar uku ko biyar ko bakwai ko tara kafin ya tafi sallar Idi.

KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Gargadi 'Yan Siyasar Kwara Kan Taron Siyasa a Filin Sallar Idi

Bukukuwan Sallah: Abubuwan 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Sani Game da Sallar Idi
Bukukuwan Sallah: Abubuwan 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Sani Game da Sallar Idi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

4. Sanya tufafi masu kyau

Sunnah ce ga musulmi ya saka tufafi sabo mai kyau.Tufafi na musamman, kuma ga maza an fi son ya kasance tufafi farare.

Idi ranar bayyana farin ciki ne da godiya ga Allah a kan ni'imar da ya yi wa bayinsa da dacewa da yin Azumi da ibadun da aka gudanar da kuma kyautar da ya samu na daren Lailatul Kadri.

5. Zikiri yayin tafiya zuwa masallacin Idi

Ana son a yi ta yin kabbara a yayin tafiya sallar Idi har idan an zauna a filin sallar Idi har zuwa liman ya zo.

Mai tafiya Sallar Idi zai dinga cewa: "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar," ko kuma ya ce "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Lailaha illahahu Wallahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil Hamd."

Ana kuma cewa: "Allahu Akbar Kabira Walhamdu lillahi kasira, Walhamdulillahi bukratan wa asila."

Za a daina kabbara idan Liman ya tayar da sallah.

6. Ba a sallar nafila a filin idi

Sallar Idi ba ta da Nafila domin ita ma Nafila ce. Amma idan a cikin masallaci ne za a yi sallar Idi watakila saboda ruwan sama, to mutum yana iya nafilar gaisuwa ga Masallaci.

Amma a filin sallar Idi ba a nafila. Mutum yana zuwa zai zauna kuma ya ci gaba da kabbara har isowar liman.

7. Sauraron huduba bayan sallar idi

Ana hudubar Idi bayan sallame Sallah. Ana son a zauna a saurari hudubar Liman, ba a son daga sallame sallah a fice.

Duk da cewa ba wajibi ba ne, amma malamin ya ce yana daga cikin alherin da Annabi SAW ya yi nuni da shi domin samun albarkar addu'ar musulmi da ake yi a cikin huduba.

8. Sauya hanyar tafiya da dawowa

Wannan Sunnah ce ta Manzo SAW ba a son a tsayar da hanya daya. Ana son mutum ya sauya hanya idan zai dawo daga sallar Idi domin zai yi wa wasu mutane na daban sallama sabanin wadanda ya yi wa sallama a lokacin tafiyarsa.

9. Yara da mata da tsoffi duka na zuwa sallar idi

Bukukuwan Sallah: Abubuwan 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Sani Game da Sallar Idi
Bukukuwan Sallah: Abubuwan 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Sani Game da Sallar Idi Hoto:Getty Images
Asali: Getty Images

Ana son dukkan al'umma su tafi idi, maza da mata da yara da tsoffi. Mata masu haila za su iya zuwa amma ba za su shiga sahu ba, za su tsaya a gefen masallaci kuma ba za su yi sallah ba.

Ana son mata idan za su tafi sallar Idi su suturta jikinsu, ka da su tafi Ibadah suna bayyana jiki kuma suna bayyana adonsu. Sannan ba a son mata su jera sahu daya da maza a filin sallar Idi. An fi son maza suna gaba mata na baya.

KU KARANTA: Da Dumi-dumi: Shugaba Buhari Ya Amince da Sabbin Matakan Tsaro a Kudancin Najeriya

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo a ranar Talata ta ce ta tura jimillar jami’anta 3200 don tabbatar da isasshen tsaro a jihar yayin da musulmai muminai ke bikin karamar Sallah, Channels Tv ta ruwaito.

A wata sanarwa da aka ba manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Orlando Ikeokwu, rundunar ta tabbatar wa al'ummar Imo cewa tana hada kai da dukkan hukumomin tsaro a jihar.

Ikeokwu ya ce ‘yan sanda sun yi shiri yadda ya kamata don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a lokacin bikin.

Yayin da yake taya musulmai murna a jihar, ya roke su da su yi amfani da lokacin domin yin addu'ar samun zaman lafiya da tsaro a jihar tare da hadin kai da zaman lafiyar kasa baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.