Muhammadu Sa'ad Abubakar
Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen inganta rayuwar yan Najeriya, inda ya ce cutar yunwa ta fi coronavirus.
A game da gambarwar sarautar Kano mun ji cewa Babban Sakataren Muhammadu Sanusi II watau Alhaji Mujtabah Abubakar Abba ya ajiye aikinsa.
A jihar Kano, har an fara hararo wanda zai iya zama Magajin Sarki Muhammadu Sanusi II. Akwai yiwuwar Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da daya daga cikin wadannan ukun.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa game da bullar annobar cutar Coronavirus a Najeriya da ma duniya gaba daya, do haka ya yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’I na musamman.
Sultan ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin taron kasa da kasa a kan soyayya da zaman tare karo na 5, wanda aka yi ma taken “Yaki da zafin ra’ayi don samar da zaman lafiya” da gidauniyar UFUK Dialogue ta shirya.
A jiya Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Zazzau murnar samun shekaru 45 a gadon mulki. Buhari ya aikowa Sarkin Zazzau sakon taya murna ne daga kasar Habasha.
A jiya ne Bishof Mathew Kukah ya soki Shugaba Buhari wajen jana’iza a Kaduna. Malamin ya ce bai taba tunani haka mulkin Buhari zai zama ba.
A jiya Sultan ya kara fitowa ya fadawa Duniya cewa Talakawa su na fuskantar tsananin rayuwa a Najeriya. Sultan ya kuma ce shugabanni su na bukatar addu’ar Talakawa domin su ci nasara.
A halin yanzu, Sultan na Sokoto, ya ce ya zoma dole a kawo karshen kisan Bayin Allah. Majalisar kolin Musulmai ta fito ta yi magana wannan karo.
Muhammadu Sa'ad Abubakar
Samu kari