Kano: Gaskiyar Magana kan Ikirarin Gwamna Ya Raba Kwanukan a matsayin Tallafi

Kano: Gaskiyar Magana kan Ikirarin Gwamna Ya Raba Kwanukan a matsayin Tallafi

  • An yi ikirarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba farantai da kwanuka ga mazauna Kano a matsayin tallafin dogaro da kai
  • A bidiyon da aka dogara da shi na ƴan daƙiƙu ya nuna Gwamna Abba Kabir Yusuf yana mika kwanuka ga mahalarta wani taro
  • Sai dai bidiyon ba shi da tsawon da zai bayar da cikakken bayani game da dalilan Gwamnan na raba kwanuka ga mahalarta taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani bidiyon Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, inda aka gan shi yana raba kwanuka ya yamutsa hazo, musamman a Kudancin Najeriya.

A cikin bidiyon mai tsawon daƙiƙa 16, an ga Gwamnan Kano yana mika farantai ga wasu mata yayin da kowa ke cikin nishadi.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kare kansa da aka tsoma shi a matsalar sace dalibai a Oyo

An riƙa yaɗa cewa Gwamna ya yi rabon tallafin Kwano a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf, a gefe guda kuma tare da yara marayu a jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Nasara Radio
Source: Facebook

Wani shafi a dandalin X mai suna The Yoruba Times ya wallafa wani gajeren bidiyo da ke nuna Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, yana raba farantai ga wasu mata da suka yi layi.

Bayan wallafa bidiyo a wannan shafi, an samj dubunnan martani da yayin da mutane sama da 280,000 suka kalla

Kano: Da gaske Abba ya raba tallafin kwano?

Binciken jaridar The Cable ta bibiyi sauran kafafen da suka wallafa irin wannan bidiyo, inda ya ci karo da shafin TikTok, mai suna @hafsatuuu2 wanda ya wallafa bidiyon tun ranar 30 ga Mayu, 2026.

Washegari, ranar 31 ga Mayu, asusun ya sake wallafa wani bidiyo daga taron, inda aka ga gwamnan yana raba farantai ga wasu yara maza yayin da aka jera nau'o'in abinci a kan tebura.

Bincike ya ƙaryata iƙirarin cewa gwamnan ya raba tallafin kwano a Kano
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a wurin wani taron siyasa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sakamakon binciken ya nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya wani taro ne domin bikin Sallah babba tare da marayu da sauran masu bukatar tallafi a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Shugaba a majalisa ya faɗi lokacin da za a amince da dokar ƴan sandan jihohi

A yayin taron ne aka rika rabon farantai ga wadanda suka halarta domin a zuba masu abincin da aka shirya.

Wannan ya saba da ikirarin cewa an ba su farantan ne a matsayin tallafin dogaro da kai kamar yadda wasu suka yada.

Gwamna bai taba tallafin kwano a Kano ba

Rahotanni da bidiyon da kafafen yada labarai suka wallafa sun nuna gwamnan yana raba farantan ne yayin da ake hidimar abinci ga marayu da masu karamin karfi.

Saboda haka, ikirarin da ke cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba farantai ga mazauna Kano a matsayin kunshin tallafin dogaro da kai ba gaskiya ba ne.

Gaskiyar abin da ya faru ita ce gwamnan ya raba farantan ne domin rabon abinci a lokacin bikin Babbar Sallah tare da marayu da sauran masu bukatar kulawa a jihar.

Kano: An karyata rabon tallafin dan kamfai

A baya, kun samu labarin cewa an yi ta yada wasu rahotanni cewa Gwamnatin Kano ce karkashin Abba Kabir Yusuf ta raba dan kamfai a wasu mata a jihar.

Kara karanta wannan

An ama daruruwan 'yan daban da suka hana jihar Kano zaman lafiya

An gano hotunan wasu mata dauke da jajayen dan kamfai wanda suke rawa da kuma tura sakonni ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wani binciken gaskiya ya ƙaryata jita-jitar cewa gwamnatin Kano ta raba kayan ga mata, an gano an yi wa hotunan da ake yadawa, inda aka gano kawai magana ce ta siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng