Me Tinubu Yake Yi da Kudaden Tallafin Man Fetur da Ya Janye? Omokri Ya Yi Bayani
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya bayyana yadda ake kashe kudaden bayan cire tallafin a gwamnatin Bola Tinubu
- Ya ce rabon kudaden FAAC ga jihohi ya karu sosai, yayin da aka kafa kwamitocin ci gaban yankuna shida tare da tallafa musu
- Omokri ya bayyana cewa an yi amfani da kudaden wajen lamunin dalibai, ayyukan manyan tituna da bunkasa rayuwar 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Reno Omokri ya yi ƙarin haske game da maganganu kan kudin da ake samu bayan cire tallafin mai da aka yi a 2023.
Fasto Omokri ya ce mutane da dama suna tambayar inda kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur suka tafi.

Source: Facebook
Tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana haka a cikin wani rubutunsa da ya yi a shafin X a yau Lahadi 14 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000
Cire tallafi: Fannonin da aka kai kuɗin
Ya ce akwai muhimman fannoni biyar da ke nuna yadda aka yi amfani da wadannan kudade.
A cewarsa, duk da ikirarin cewa an bar dala biliyan 14, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta daga ajiyar kudaden waje zuwa dala biliyan 50.26 zuwa ranar Litinin, 8 ga Yunin 2026.
Omokri ya ce irin wannan ajiyar kudaden waje tana taimakawa wajen kare tattalin arziki daga rugujewar kasuwanci, biyan bukatun shigo da kayayyaki daga kasashen waje da kuma tabbatar da lamunin kasa.
Ya kara da cewa jihohin Najeriya yanzu suna karbar fiye da ninki biyu, wasu ma fiye da haka, idan aka kwatanta da abin da suke samu a lokacin gwamnatin Buhari.
Misali, ya ce a watan Maris na 2022, FAAC ta raba jimillar Naira biliyan 725.571 ga matakan gwamnati uku, amma a watan Maris na 2026 an raba Naira tiriliyan 2.036.
Ya kuma ce a karkashin gwamnatin Tinubu, dukkan yankunan siyasar Najeriya guda shida yanzu suna da kwamitocin bunkasa yankuna da ke samun tallafin gwamnati.
Wadannan sun hada da Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas, Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Hukumar Raya Yankin Neja Delta.
A cewarsa, wadannan hukumomi suna karbar kusan Naira tiriliyan 2.5 a kowace shekara, kudaden da ba sa samu a zamanin gwamnatin Buhari saboda yawancinsu ba su wanzu ba.

Source: Facebook
Yadda aka tallafawa ɗalibai a Najeriya
Omokri ya ce sama da dalibai miliyan daya marasa karfi suna cin gajiyar kusan Naira biliyan 300 ta shirin lamunin karatu na NELFUND karkashin manufofin Renewed Hope.
Ya kuma yabawa gwamnatin Tinubu kan ayyukan manyan tituna da ake gudanarwa a fadin kasar nan lokaci guda domin hada yankuna daban-daban.
Har ila yau, ya ambaci aikin titin Lagos zuwa Calabar mai tsawon kilomita 750 da kudinsa ya kai Naira tiriliyan 15, wanda ke hada Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu.
Sannan ya ce ana aikin titin Illela zuwa Sokoto zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1,068 da kudinsa ya kai Naira tiriliyan 13 domin hada Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma.
Haka kuma, ana gina titin Trans-Saharan mai tsawon kilomita 465 da aka kiyasta kudinsa dala miliyan 750 domin hada Kudu maso Gabas da yankunan Arewa.

Kara karanta wannan
Mele Kyari: Kwamitin majalisa ya umarci cafke tsohon shugaban NNPCL kan badakalar N210trn
Ya ce wadannan su ne wasu daga cikin hanyoyin da ake ganin an yi amfani da kudaden da aka samu bayan kawo karshen tallafin man fetur.
Omokri ya kara da cewa kafin gwamnatin Tinubu ta kama aiki, Najeriya na da karancin ajiyar kudaden waje kuma jihohi da dama suna bin ma'aikata albashi na watanni.
Omokri ya magantu kan daukar nauyin Boko Haram
Mun ba ku labarin cewa tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Fasto Reno Omokri, ya karyata zargin cewa gwamnati na daukar nauyin Boko Haram.
Omokri ya kalubalanci wani sanatan Amurka, yana mai cewa ya kawo hujjojin da ke tabbatar da zargin idan yana da gaskiya.
Wani shugaban gari a Amurka ya goyi bayan Omokri, inda ya yarda gwamnatin Najeriya ba ta da hannu a ayyukan Boko Haram.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
