Mujtabah Abba ya yi murabus daga Falakin Kano ya bar Masarauta

Mujtabah Abba ya yi murabus daga Falakin Kano ya bar Masarauta

Mun samu labari cewa Mai girma Falakin Birnin Kano, Alhaji Mujtabah Abubakar Abba ya yi murabus daga kan kujerar da ya ke kai ta Falaki.

Mujtabah Abubakar Abba ya rubuta wasika ta musamman ga Sakataren majalisar Kano inda ya sanar da shi game da ajiye rawaninsa da aikinsa.

Alhaji Mujtabah Abubakar Abba ya bayyana cewa ya sauka daga matsayin da ya ke kai na babban Sakataren tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II.

Bugu da kari, Basaraken ya sauka daga sarautar Falaki wanda tsohon Sarkin Birni Muhammadu Sanusi II ya nada sa bayan ya hau gadon mulki.

Tsohon Falakin na Birnin Kano ya gode da aka ba shi dama ya rike wannan sarauta a fadar Kano. Falakin ya rubuta wannan wasika ne a jiya Litinin.

KU KARANTA: Aminu Ado Bayero: Wasu hotunan sabon Sarkin Kano da aka nada

Haka zalika tsohon Falakin ya nuna godiya ga Ma’aikatan masarautar Birnin Kano da su ka ba shi hadin-kai a tsawon lokacin da ya yi aiki tare da su.

Sai dai Legit.ng ba ta da labarin ko Sakataren fadar Sarkin Birnin na Kano watau Galadima Alhaji Abbas Sanusi ya yi na’am da wannan murabus na sa.

Idan ba ku manta ba Malam Muhammadu Sanusi II ya nada Mujtabah Abubakar Abba a matsayin Sakatarensa ne bayan ya tsige Isa Sanusi Bayero.

Ana zargin Alhaji Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot ya na cikin wadanda su ka rika fallasa wasu sirrin masarautar a lokacin tsohon Sarki.

A daidai wannan lokaci kuma mun kuma samu labari cewa Shamakin Kano ya sayawa sabon Sarkin Birni, Aminu Ado Bayero sabuwar motar hawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel