Cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da Coronavirus - Sultan

Cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da Coronavirus - Sultan

- Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen inganta rayuwar yan Najeriya

- Sultan na Sokoto ya ce lallai cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da mummunan cutar Coronavirus

- Ya ce a matsayin su na Shugabannin addinai da al’umma, ya zama dole su tattauna wadannan lamura, da kuma ba gwamnati shawarwari

Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen inganta rayuwar yan Najeriya, inda ya ce lallai cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da mummunan cutar Coronavirus.

Sultan wanda ya yi magana a taron kungiyar addinai na Najeriya a Abuja, a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris, ya ce duk da cewar Coronavirus na kashe daruruwan mutane a fadin duniya, “cutar yunwa” shine babban makashinyan Najeriya.

Cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da Coronavirus - Sultan
Cutar yunwa na kashe yan Najeriya fiye da Coronavirus - Sultan
Asali: UGC

Ya ce: “Akwai wata babbar cuta da ke kashe yan Najeriya fiye da Coronavirus. Wannan cutar ita ce yunwa. Akwai cutar yunwa kuma ta yi lamari. Akwai bukatar ku zaga kauyuka da garuruwa ku ga yadda mutane ke gwagwarmayar rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi

“Wadannan muhimman lamura ne, kuma a matsayin mu na Shugabannin addinai da al’umma, ya zama dole mu tattauna wadannan lamura, da kuma ba gwamnati shawarwari da duba yadda gwamnati za ta aiwatar da shawarwarin."

A wani labarin kuma mun ji cewa, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya gargadi yan Najeriya su rage halin musafaha da runguman juna domin takaita yaduwar annobar Coronavirus da ta addabi duniya.

Ministan ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da fara wani gini a unguwar Karshi dake Abuja ranar Alhamis.

Ministan ta yayi kira ga yan Najeriya su rika nesa-nesa da juna kuma su guji wuraren da akwai cincirindon mutane.

Ministan ya shawarci yan Najeriya su rika gaisawa ta hanyar durkusa da daura hannu a kirji.

Aregbesola ya kara da cewa annobar Coronavirus ta zama babbar annoba ga duniya kuma idan ba a dau mataki ba za ta zama mana babbar kalubale.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng