A fita neman jinjirin watan Sha’aban – Sultan Sa’ad ga Musulmai

A fita neman jinjirin watan Sha’aban – Sultan Sa’ad ga Musulmai

Mai alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga al’ummar Musulman Najeriya da su fita neman jinjirin sabon watan Musulunci na Sha’aban, shekarar Musulunci 1441 bayan Hijirar Annabi Muhammadu (S.A.W)

Sultan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 28 ga watan Rajab, cikin wata sanarwa dake dauke da sa hannun shugaban kwamitin dake baiwa Sultan shawara a kan harkokin addinin, Farfesa Sambo Junaid.

KU KARANTA: Majalisar koli ta Musulunci ta bada umarnin kulle Masallatan Abuja saboda Coronavirus

Sanarwar ta bayyana cewa ana kira ga Musulmai da su fita neman jinjirin watan Sha’aban daga ranar Talata, 29 ga watan Rajab, wanda ya yi daidai da 24 ga watan Maris, haka zalika an yi kira ga duk wanda ya ga watan ya shaida ma dakaci mafi kusa da shi, ko hakimi domin a sanar ma Sultan.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito watan Sha’aban shi ne wata na 8 a jerin watannin Musulunci, wanda daga shi sai wata mai alfarma, watan azumin Ramadana.

A wani labarin kuma, majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya, NSCIA, dake karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ta bayar da umarnin garkame dukkanin masallatan dake babban birnin tarayya Abuja a dalilin cutar Coronavirus.

Daraktan mulki na majalisar, Yusuf Nwoha ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, 23 ga watan Maris, inda yace majalisar na umartar duk Musulmi ya yi sallars a gida don kauce ma yaduwar cutar.

Idan za’a tuna a ranar Litinin ne hukumar gudanarwa ta babban Masallacin Abuja ta sanar da daukan matakin garkame Masallacin a kokarinta na yaki da yaduwar annobar Coronavirus.

Nwoha yace majalisar NSCIA ta yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa da tsakanin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da wasu zababbun Maluman addinin Musulunci.

Sanarwar ta kara da yin kira ga Musumai da su hada hannu da gwamnatin tarayya wajen yaki da wannan mugunyar cuta mai toshe numfashi domin a samun nasarar kawar da ita a kasar gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel