Za mu ga bayan Boko Haram da ikon Allah – Sultan ya baiwa yan Najeriya tabbaci

Za mu ga bayan Boko Haram da ikon Allah – Sultan ya baiwa yan Najeriya tabbaci

Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban majalisar koli ta Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya baiwa yan Najeriya tabbacin Najeriya za ta samu nasara a yakin da take yi da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram duk da halin da ake ciki.

Sultan ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin taron kasa da kasa a kan soyayya da zaman tare karo na 5, wanda aka yi ma taken “Yaki da zafin ra’ayi don samar da zaman lafiya” da gidauniyar UFUK Dialogue ta shirya.

KU KARANTA: Hukuncin kisa: Maryam Sanda ta kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara

Daily Trust ta ruwaito, Sultan, wanda ya samu wakilcin Sarkin Jiwa, Dakta Idris Musa ya bayyana cewa yawancin yan Najeriya basu kaunar junansu, sa’annan ya koka kan kashe kashe da zubar da jini da ake yi a Najeriya, inda yace matsalar ta kai ga mai kudi yana gudun talaka.

Don haka ya bukaci yan Najeriya su zauna lafiya da junansu, kuma su kasance masu kaunar abokansu, kuma Musulmai su kaunaci yan uwansu Kiristoci domin Allah Ya kallemu da idon rahama, Ya dawo mana da zaman lafiya a Najeriya.

“Qur’ani sako ne ga al’umma baki daya, Bibul ma haka, idan har ba zamu iya sauraron abinda Qur’ani da Bibul suke fada man aba, muka cigaba da zama a halin da muke ciki, me muke tunanin zai faru? Wannan na daga cikin kudar da Allah Yake dandana mana saboda zunubbanmu, idan zamu tuba mu koma ga Allah, komai zai sauya.” Inji shi.

Sa’annan ya bayyana farin cikinsa da godiya ga gidauniyar UFUK saboda kokarin da suke yin a hada kan al’ummar duniya su zamto daya, kuma su kaunaci junansu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

A nasa jawabin, shugaban UFUK, Kamil Kemanci ya bayyana cewa manufar kungiyar shi ne samar da zaman lafiya, soyayya, zaman lafiya, tausayi, girmama juna da mutunta dan adam domin samar da al’umma kyakkyawa.

Kamil ya yi kira ga gwamnati ta hada hannu da mazauna unguwanni wajen yaki da ta’addanci ta hanyar dakile hanyoyin da kungiyoyin ta’addanci suke daukan mayaka daga cikin matasa, inda yace gwamnati ta samar da tsarin gano ire iren matasan nan ta hana su shiga hanyar halaka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel