Jerin wadanda ake tunanin za su samu sabuwar sarautar Birnin Kano

Jerin wadanda ake tunanin za su samu sabuwar sarautar Birnin Kano

Bayan an tunbuke Muhammadu Sanusi II daga sarautar Birnin Kano, an fara magana game da wanda ake sa ran zai karbi wannan babbar kujera na gidan Dabo an jima.

BBC Hausa sun kawo jerin wasu manyan masu rike da sarauta uku a Kano da ake tunanin a cikinsu ne Masu nada sarki da gwamnatin Kano za su zabi Magajin Sanusi II.

1. Abbas Sanusi (Galadiman Kano)

Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya na cikin wadanda ake ganin zai iya zama sabon Sarkin Birni. Galadiman Birnin shi ne wanda ya fi kowa matsayi yanzu a fadar Sarki bayan Waziri.

Abbas Sanusi Mahaifi ne a wajen Muhammadu Sanusi II, kuma ya na cikin manyan ‘Ya ‘yan Sarki Sanusi I wanda ya fara nada shi Hakimi a Ungogo kuma Sarkin-Dawakin Tsakar Gida a 1959.

Bayan nan Abbas Sanusi ya rike sarautar Dan Iyan Kano da Wamban Kano. Abbas ya yi aiki da Sarakuna hudu. Sai dai kuma ganin yawan shekarunsa, akwai yiwuwar ba zai samu mulkin ba.

2. Nasiru Ado Bayero (Ciroman Kano)

Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda shi ne ‘Dan Sarki Ado Bayero na uku a Duniya ya na cikin wadanda ake yi wa hangen wannan gadon sarauta. Nasiru Ado shi ne Hakimin Nasarawa a Birni.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje zai nada sabon Sarki a Birnin Kano

Jerin wadanda ake tunanin za su samu sabuwar sarautar Birnin Kano

Ana tunanin Magajin Sanusi II zai fito daga gidan Marigayi Ado Bayero
Source: Twitter

Sarki Sanusi II ne ya nada Amininsa kuma ‘Dan Marigayi Sarki Bayero a matsayin Ciroman Kano. Nasiru Bayero ya karbi rawanin ‘Danuwansa Sanusi Bayero wanda ya ki yi wa Sanusi mubaya’a.

Nasiru Bayero babban ‘Dan kasuwa ne kuma Attajiri wanda ya ke da ilmin boko na zamani wayewar Duniya. Kafin yanzu ya rike Turakin Kano. Ciroma ya yi aiki har a kasar Ingila.

3. Aminu Ado Bayero (Sarkin Bichi)

Akwai yiwuwar Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da Mai martaba Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Birni. Aminu Ado shi ne ‘Dan Marigayi Ado da ke rike da kasa a yanzu.

Tsohon Wamban na kasar Kano ya san gidan sarautar da ya tashi. Kafin yanzu ya rike Sarkin Dawakin tsakar gida. Bayan rasuwar Tijjani Baba Hashim, Sanusi II ya nada shi sabon Wambai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel