Sa'ad Abubakar ya koka da halin da ‘Yan kasa su ke ciki, ya bukaci addu’o’i

Sa'ad Abubakar ya koka da halin da ‘Yan kasa su ke ciki, ya bukaci addu’o’i

Mai alfarama Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga shugabannin Najeriya su kara kokarin wajen ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki a yau.

Sultan din kasar Sokoto ya yi wannan kira ne a Ranar Asabar, 8 ga Watan Fubrairun 2020 wajen bikin taya Sarkin Zazzau cika shekaru 45 a kan gadon mulki.

A karshen makon nan ne Mai martaba Shehu Idris ya yi bikin cika shekaru 45 a kan sarauta. Sarkin Musulmai ya halarci wannan gagarumin biki da aka yi.

“Mun zo nan ne domin mu yi wa Sarki addu’ar samun kyakkyawar karshe da rokon Ubangiji ya ba shi ladar shugabancin da ya ke yi Zazzau da daukacin kasa.”

“Don haka mun godewa Malamanmu su ka tunatar da mu game da komawa Ubangiji a duk lokacin da mu ka samu kanmu cikin halin kunci” Inji Sultan

KU KARANTA: Kashe-kashen da ake fama da shi ya faye yawa - Sultan

Sa'ad Abubakar ya koka da halin da ‘Yan kasa su ke ciki, ya bukaci addu’o’i
Sultan ya ce Shugabanni su na bukatar addu’ar Talakawa domin su ci nasara
Asali: UGC

Mai alfarma Sultan ya yabawa shawarar Malamai, ya ke cewa: “Mun dauki wadannan nasiha da su ka yi mana. Sun zama sanadin samun natsuwar zuciyar mu.”

Sultan ya kara da cewa: “Mu na kira ga shugabanninmu su ji-kan Talakawa. Kowa ya san ana cikin hali na wahala. Babu abin da ya gagari ikon Ubangiji Allah.

"Na mu shi ne mu cigaba da addu’a, mu kuma yi wa shugabanninmu addua’a. Mutanen Zariya, ku tashi tsaye da yi wa shugaban kasa da gwamnan Kaduna addua’a.”

Sarkin Musulmai ya bukaci jama’an Garin Zariya su sa duka shugabanninsu na kowane mataki cikin addu’a. Ya ce: “Ka da ku kyale mu da iyawarmu da kwarewarmu.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng