Muharram: Sarkin Musulmi Ya Umarci Al'umma kan Duba Jinjirin Watan Sabuwar Shekara

Muharram: Sarkin Musulmi Ya Umarci Al'umma kan Duba Jinjirin Watan Sabuwar Shekara

  • Sarkin Musulmi ya umarci daukacin Musulman Najeriya su fito domin neman ganin jinjirin watan Muharram 1448AH
  • Ya bukaci duk wanda ya tabbatar da ganin jinjirin ya sanar da hakimi ko shugaban ƙauyensu mafi kusa domin isar da rahoto zuwa Majalisar Masarautarsa
  • Sakamakon wannan aiki ne zai tantance ranar fara sabuwar shekarar Musulunci a Najeriya, tare da tabbatar da haɗin kai wajen gudanar da ibadu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci fara duba jinjirin wata.

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Ƙungiyar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya bukaci Musulmi su fara neman ganin jinjirin watan Muharram 1448AH.

Sarkin Musulmi ya ba umarni kan duban wata
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Facebook

An bayyana wannan umarni ne cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Wali Junaidu, shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Masarautar, ya fitar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yadda aka birne Janar Rabe da ya rasu a hannun 'yan bindiga cikin jimami a Katsina

Umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar

Sanarwar ta ce ranar Litinin, 15 ga Yunin 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga Zulhijjah 1447AH, ita ce ranar da aka ware domin neman ganin jinjirin watan Muharram a fadin Najeriya.

Sarkin Musulmin ya bukaci Musulmai su lura da sararin sama bayan faduwar rana tare da kai rahoton duk wani sahihin gani ta hanyoyin gargajiya da aka tanada.

Ya ce duk wanda ya tabbatar da ganin jinjirin ya sanar da Hakimi ko shugaban ƙauyen da ke kusa da shi domin a isar da bayanin zuwa Majalisar Masarautar Sokoto da kuma gare shi.

Ana amfani da wannan aikin neman jinjiri duk shekara wajen tantance farkon watannin Musulunci, kuma ana kallonsa a matsayin muhimmiyar ibada ga Musulmai a Najeriya.

An umarci fara duba jinjirin watan Muharram
Taswirar jihar Sokoto da fadar Sarkin Musulmi ta ke. Hoto: Legit.
Source: Original

Muhimmancin watan Muharram a Musulunci

Watan Muharram na da matsayi na musamman a Musulunci domin yana cikin watanni huɗu masu alfarma, kuma shi ne farkon kalandar Musulunci da ake amfani da ita wajen tsara muhimman ibadu.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi maganar mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan Bindiga

Sakamakon neman jinjirin ne zai zama tubalin sanar da ranar farko ta Muharram 1448AH da kuma fara sabuwar shekarar Musulunci ga Musulman Najeriya, cewar Vanguard.

Shugabannin addini sun saba ƙarfafa jama'a su shiga wannan aiki, suna jaddada muhimmancin tabbatar da sahihancin rahotanni da bin hanyoyin da aka amince da su.

Ana sa ran Majalisar Masarautar Sokoto za ta sanar da matsayinta na hukuma kan fara watan Muharram bayan tattara da tantance rahotannin da za su fito daga sassa daban-daban na ƙasar.

Wannan sanarwa ta zo ne yayin da Musulmai ke shirin tarbar sabuwar shekarar Musulunci, lokaci da ake yawan yin tunani, addu'o'i da sabunta ƙudurin kusantar Allah.

Sultan ya magantu kan jita-jitar Musuluntar da Najeriya

An ji cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya musanta rade-radin cewa ana shirin musuluntar da Najeriya.

Sultan ya jaddada cewa Musulmi ba su da wata manufa ta kawar da Kiristoci, yana mai cewa Allah cikin hikimarsa ya hada addinan biyu a wuri daya.

Sarkin ya kuma yi Allah-wadai da danganta laifuffukan ta’addanci da addini, yana mai cewa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba su da alaka da musulmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.