Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero sun ziyarci Sanusi Ado Bayero

Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero sun ziyarci Sanusi Ado Bayero

Mun samu labari cewa Sarakunan kasar Bichi da Kano watau Nasiru Ado Bayero da Aminu Ado Bayero sun hadu da Alhaji Sanusi Ado Bayero.

Sababbin Sarakunan sun hadu da ‘Danuwansu ne yayin da su ka kai masa ziyara a gidansa. Sarakunan sun kai ziyarar ne a farkon makon nan.

Wannan labari ya zo gare mu ne ta wani bidiyo da aka wallafa a shafin Masarautar Kano da ke dandalin sadarwa na zamani na Tuwita a jiya.

Shafin @HrhBayero su kan dauko labaran da su ka shafi Masarautar Kano ta Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero tun bayan da yau kan gadon mulki.

A bidiyon an bayyana cewa Sarakunan sun tashi da kafafunsu ne sun kai wa babban Yayan na su ziyara a gidansa da ke cikin Birnin Kano a jihar.

KU KARANTA: Sarkin Kano Aminu Bayero ya yi jawabi game da cutar COVID-19

Bisa dukkan alamu an dauki lokaci tsohon Ciroman ba ya kasar Kano. Legit.ng Hausa ta na tunanin wannan ne karon farko da Sarakan su ka hadu.

Idan ba ku manta ba tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne ya tubewa Sanusi Lamido Ado Bayero rawanin Ciroman Kano bayan ya hau mulki.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya zargi Takwaransa Sanusi Ado Bayero da kin yi masa mubaya’a bayan dukkansu sun nemi kujerar Sarkin Kano a 2014.

Sanusi Bayero ya rasa kujerar sa ne wajen ‘Danuwansa bayan rasuwar Mahaifinsu Ado Bayero. Daga baya aka karbe sarautarsa aka ba Nasiru Bayero.

Bayan shekaru kusan hudu ne gwamnatin Kano ta tunbuke Mai martaba Muhammadu Sanusi II, ta maye gurbinsa da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero.

A dalilin haka ne Ciroma Nasiru Ado Bayero ya samu sarautar Bichi. Yanzu dukkansu sun zo sun gaida Yayan na su, sai dai ba a ji abin da su ka tattauna ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel