Buhari: A sa dokar ta-baci a kan harkar tsaro a Najeriya Inji NSCIA
Majalisar kolin harkar musulunci a Najeriya, NSCIA, ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa dokar ta-baci a kan sha’anin tsaro a fadin kasar.
NSCIA ta yi wannan kira ne ta bakin shugabanta kuma Sultan na kasar Sokoto watau Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III.
Mai alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi wannan kira ne a jiya Ranar Laraba a wajen wata zantawa da Manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Sarkin Musulman ya koka da cewa kusan duk ranar Duniya sai an samu aukuwar garkuwa da mutane ko kuma fashi da makami ko wani mugun harin.
Muhammad Sa’ad Abubakar III ya kuma koka game da yadda ake amfani da Bayin Allah wajen aikin tsubbu a bangarori da-dama na fadin kasar nan.
KU KARANTA: Buhari ya kaddamar da wasu jiragen yaki a Najeriya
Alhaji Aselemi Ibrahim, Yusuf Chinedozi Nwoha, da kuma Farfesa Salisu Shehu su ne su ka sa hannu a wannan jawabi a madadin kungiyar NSCIA.
Chinedozi Nwoha wanda shi ne shugaban yada labarai da sadarwa na NSCIA ya karanto da wannan jawabi na Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar.
Majalisar ta bayyana cewa halin da aka shiga na rashin tsaro ya kai wani hali da ya zama dole a fito a yi magana, kuma a dauki matakin kafa dokar ta-baci.
Nwoha a madadin NSCIA ya ce: “Halin da ake ciki yau a Najeriya ya kai inda ya kai, wannan yanayi ya na bukatar matakin gaske domin kare ‘yan kasa.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng