Annobar Coronavirus: Sultan ya bukaci Musulmai su fara addu’o’in neman agaji daga Allah

Annobar Coronavirus: Sultan ya bukaci Musulmai su fara addu’o’in neman agaji daga Allah

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa game da bullar annobar cutar Coronavirus a Najeriya da ma duniya gaba daya, do haka ya yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’I na musamman.

Jaridar Punch ta ruwaito Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Jama’atil Nasril Islam, JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya fitar a ranar Laraba, 4 ga watan Maris a garin Kaduna.

KU KARANTA: Miyagun yan bindiga sun bude ma jama’a wuta, sun kashe Yansanda 2, wani guda 1

Sultan ya yi kira ga Musulmai su dage da tsafta tare da bin duk wasu hanyoyin tsaftace kawunansu don kauce ma yada cutar Coronavirus, sa’annan ya yi kira ga Malamai da limamai su cigaba da wayar da kawunan jama’a akan cutar a dukkanin salloli biyar na kowanne rana.

“Mun damu kwarai game da yaduwar mugunyar annobar cutar Coronavirus, kuma mun damu da barazanar da yake ma yi ma dan Adam, baya ga kasar China inda cutar ta bulla, ta shiga kasashe da dama kamar nahiyar Turawa, Amurka, yankin Asia, da kuma Najeriya.

“Kowacce kasa na daukan matakan kiyaye yaduwar cutar ta hanyar killace wadanda ake zaton sun kamu da ita, yayin da wadanda gwaje gwaje suka tabbatar sun kamu kuma suke samun kulawa a cibiyoyin kiwon lafiya na musamman.

“Don haka wajibi ne dukkanin limamin Masallatan kamsu salawati da limaman Masallacin Juma’a su wayar da kawunan jama’ansu game da illar cutar, kuma su nanata ma jama’a tare da jaddada musu muhimmancin daukan matakan kare kai ta hanyar tsaftace kansu da muhallansu.

“Haka zalika JNI na kira ga limaman Masallatai su fara gudanar da addu’o’i na musamman domin rokon Allah Ya kawo karshen wannan cutar tare da duk wasu cututtuka da suka addabi duniya gaba daya.” Inji shi.

Daga karshe mai alfarma sarkin Musulmi ya yi kira ga hukumomin kiwon lafiya da aikin kare yaduwar cutar ya rataya a wuyarsu su tabbata sun yi aikinsu tukuru ta yadda za’a shawo kan cutar dsa wuri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel