Iran da Amurka Sun Cimma Yarjejeniya, Farashin Mai Ya Fara Sauka Kasa

Iran da Amurka Sun Cimma Yarjejeniya, Farashin Mai Ya Fara Sauka Kasa

  • Shugaba kasa Donald Trump ya ce Amurka da Iran sun cimma yarjejeniya domin sake buɗe mashigar ruwan Hormuz da Tehran ta rufe
  • Kasuwannin hada-hadar hannayen jari na Amurka da manyan kasuwannin Asiya sun yi tashin gwauron zabi, yayin da farashin mai ya faɗi
  • Rufe mashigar Hormuz ya haifar da ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka taɓa addabar kasuwannin man fetur na duniya a tarihi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Amurka da Iran sun amince da wata yarjejeniya domin kawo ƙarshen yaƙi a tsakaninsu, lamarin da ya kawar da babban cikas ga kasuwanni tare da sa farashin mai ya ragu.

Donald Trump ya ce Amurka da Iran sun cimma yarjejeniya domin sake buɗe mashigar ruwan Hormuz, abin da ke nuna yiwuwar kawo ƙarshen rikicin makonni 15 da ya kawo cikas ga samar da man fetur a duniya.

Kara karanta wannan

"Ba ciwon suga ba ne": Yaron Janar Rabe ya fallasa abin da ya yi zargin ya kashe mahaifinsa

Mojtaba Khamenei da Donald Trump
Ayatollah Mojtaba Khamenei a hagu da Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Biyo bayan lamarin, Al Jazeera ta wallafa cewa Iran ta ce yaƙi da ayyukan soji a dukkan bangarori, ciki har da Lebanon, za su ƙare gaba ɗaya daga daren Litinin, 15 ga Yunin 2026.

Farashin danyen mai ya sauka

Farashin mai ya faɗi, yayin da kasuwannin hannayen jari suka yi tashin gwauron zabi bayan bayyana labarin yarjejeniyar Iran da Amurka.

Rahoto ya nuna cewa farashin gangar ɗanyen man Brent na duniya ya ragu da kashi 4.2 cikin 100 zuwa $83.73.

Farashin ɗanyen man West Texas Intermediate (WTI) na Amurka kuwa ya ragu da kashi 4.8 cikin 100 zuwa $80.77 a kowace ganga.

Kasuwannin hannayen jari na Amurka sun tashi, inda na S&P 500 suka ƙaru da kashi 1.1 cikin 100, na Dow suka ƙaru da kashi 0.8 cikin 100, yayin da na Nasdaq suka yi tsalle da kashi 1.8 cikin 100.

Kasuwannin duniya ma sun yi tashin gwauron zabi, inda kasuwar Nikkei 225 ta Japan ta tashi da kashi 5.4 cikin 100, yayin da Kospi ta Koriya ta Kudu ta tashi da kashi 4.9 cikin 100.

Kara karanta wannan

Duniya za ta huta: Trump ya ce yaki da Iran ya zo karshe, babu sauran kai hari

Bayanin Trump kan yarjejeniyar

A daren Lahadi, 14 ga watan Yunin 2026 shugaba Donald Trump ya sanar da cewa ya bayar da izinin dakatar da cire shinge da suka sa wa Iran.

“Yarjejeniyar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran yanzu ta kammala,”

In ji Trump kamar yadda Business Insider Africa ta wallafa.

“Ina ba da cikakken izini a buɗe mashigar Hormuz ba tare da wani kuɗin haraji ba, kuma a lokaci guda ina ba da umarnin cire katangar jiragen ruwan yaƙin Amurka nan take.”
Hanyar Hormuz da ke Iran
Mashigar Hormuz da ake takaddama a kanta a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanin da Pakistan da Iran

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, wanda ya shiga tsakani a tattaunawar, ya ce za a gudanar da bikin sanya hannu a hukumance a ranar 19 ga Yunin 2026.

Iran ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wata takardar fahimtar juna kan tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin da suka yi da Amurka/Isra'ila.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce bangarorin biyu za su yi amfani da tsagaita wutar kwanaki 60 domin tattauna wata faffadar yarjejeniya.

Kara karanta wannan

Yadda aka sulale da sinadarin hada nukiliya a asirce daga Venezuela zuwa Amurka

An kai hari Amurka an kashe rai

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani dan bindiga dadi ya kai hari kasar Amurka inda ya kashe mutum daya ya jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin da ya kai harin ya shafe sa'o'i akalla biyu yana arabganyda jami'an tsaro kafin a yi nasarar kashe shi.

Dan bindigar ya kai harin ne a daidai lokacin da ƙasashe da dama suka taru a Amurka domin gasar kofin duniya ta shekarar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng