Shugaban kasa ya taya Sarkin Zazzau murnar samun shekaru 45 a gadon mulki

Shugaban kasa ya taya Sarkin Zazzau murnar samun shekaru 45 a gadon mulki

Shugaban kasa Muhammadu ya taya Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, murna na cika shekar 45 ya na kan gadon mulkin sarautar Zazzau.

Muhammadu Buhari ya aikowa Sarkin da wannan sako ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Faemi Adesina, wanda ya fitar da wani gajeren jawabi a jiya.

Jawabin shugaban kasar Najeriyar ya bayyana Sarkin da Limamin zaman lafiya da kwanciyar hankali da aminci, kuma mai kowawa mutanesa cigaba.

Buhari ya bayyana cewa Sarkin na 18 a tarihin kasar Zazzau kuma shugaban Sarakunan Kaduna, haske ne kuma matattarar tarihi da al’adun masarauta.

A cewarsa, Shehu Idris, Sarki ne Mai daraja wanda gwamnatin tarayya da ta jiha ta shafe shekara da shekaru ta na amfana da shawarwarinsa na manya.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Mai martaba Sarki Shehu Idris na Zariya

Shugaban kasa ya taya Sarkin Zazzau murnar samun shekaru 45 a gadon mulki
Buhari ya aikowa Sarkin Zazzau sakon taya murna daga kasar Habasha
Asali: Twitter

Har ila yau, shugaba Muhammadu Buhari, ya yi kira ga Mai martaba da ya cigaba da jajircewa yadda ya saba na kokarin kawo zaman lafiya a kasa.

Buhari ya bukaci Sarkin ya dage wajen ganin kasar Zazzau ta zama abin koyi na zaman lafiya a fadin Najeriya, kamar yadda jawabin ya bayyana.

Bayan haka, Muhammadu Buhari ya yi addu’a ga Ubangiji ya karawa wannan Sarki lafiya da basirar da zai cigaba da yi wa al’ummar kasarsa hidima.

Sarki Shehu Idris ya hau gadon mulki a 1975, ya shafe shekaru 45 ya na sarauta. Wannan ya sa ya zama Sarkin da ya fi dadewa ya na mulki a Zariya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel