Majalisar koli ta Musulunci ta bada umarnin kulle Masallatan Abuja saboda Coronavirus

Majalisar koli ta Musulunci ta bada umarnin kulle Masallatan Abuja saboda Coronavirus

Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya, NSCIA, dake karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ta bayar da umarnin garkame dukkanin masallatan dake babban birnin tarayya Abuja a dalilin cutar Coronavirus.

Premium Times ta ruwaito Daraktan mulki na majalisar, Yusuf Nwoha ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, 23 ga watan Maris, inda yace majalisar na umartar duk Musulmi ya yi sallars a gida don kauce ma yaduwar cutar.

KU KARANTA: Annobar Corona: Bankin Access ta garkame ofishinta a Legas bayan bullar cutar

Idan za’a tuna a ranar Litinin ne hukumar gudanarwa ta babban Masallacin Abuja ta sanar da daukan matakin garkame Masallacin a kokarinta na yaki da yaduwar annobar Coronavirus.

Nwoha yace majalisar NSCIA ta yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa da tsakanin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da wasu zababbun Maluman addinin Musulunci.

Sanarwar ta kara da yin kira ga Musumai da su hada hannu da gwamnatin tarayya wajen yaki da wannan mugunyar cuta mai toshe numfashi domin a samun nasarar kawar da ita a kasar gaba daya.

Daga karshe yace kulle masallaci ba wani sabon abu bane a Musulunci, domin kuwa a zamanin Annabi Muhammad (S.A.W) an taba samun haka, don haka ya nemi goyon bayan Limamai domin tabbatar da bin wannan umarni.

A wani labarin kuma, masana kiwon lafiya a kasar Birtaniya, kwararru a sashin Kunne, Hanci da Makogwaro sun gano wasu sabbin alamomin cutar Coronavirus, daga ciki akwai daina jin dandano a harce da kuma daina gane kamshi ko wari.

Kungiyar likitocin Kunne, Hanci da Makogwaro na kasar Ingila ne suka sanar da haka, inda suka ce wadannan alamomi suna bayyana ne a inda sanannun alamomin cutar basu bayyana a jikin mai dauke da kwayar cutar ba.

Don haka suka ce duk mara lafiyan dake fama da wadannan matsaloli biyu, akwai yiwuwar yana dauke da cutar Coronavirus, saboda an samu ire iren mutanen nan a kasashen China da Kudancin Koriya, inda suka kira alamomin ‘Anosmia.’

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel