Annobar Corona: Sultan ya bayyana bacin rai da yadda gwamnoni suka bude wuraren ibada

Annobar Corona: Sultan ya bayyana bacin rai da yadda gwamnoni suka bude wuraren ibada

Majalisar koli ta shari’ar Musulunci, NSCIA, karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, ta bayyana damuwarta da yadda gwamnoni suka bude Masallatai da coci-coci.

Majalisar ta ce gwamnonin sun bude duk da sanin cewa tarukan jama’a na taimakawa wajen rura yaudwar cutar nan mai toshe numfashi wato Coronavirus.

KU KARANTA: Mutane 5 sun sake kamuwa da annobar Coronavirus a Najeriya, jimilla 323

Annobar Corona: Sultan ya bayyana bacin rai da yadda gwamnoni suka bude wuraren ibada
Annobar Corona: Sultan ya bayyana bacin rai da yadda gwamnoni suka bude wuraren ibada
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito an garkame masallatai da coci-coci a sassan kasar ne domin kare yaduwar cutar, amma a karshen makon da ta gabata wasu gwamnonin sun sake budesu.

NSCIA ta bayyana wannan matakin sake bude Masallatai da sauran wuraren bauta a matsayin abin takaici, kamar yadda daraktan watsa labaru, Yusuf Chinedozie Nwoha ya bayyana.

Nwoha ya bayyana haka ne yayin rabon kayan tallafi ga jama’an Mpape a Abuja, inda yace: “Wannan abin takaici ne musamman tun da dai har yanzu ba’a samu maganin Coronavirus ba.

“NSCIA na rokon yan Najeriya, mun san yan Najeriya suna da taurin kai wani lokaci, amma ku kare kanku don ku taimaka ma wasu su tsira da ransu. A yau mun kawo tallafi ne ga magidanta 90 a Mpape.

“Idan har jama’a sun san girman matsalar da muke fuskanta, da kansu za su zauna a gida ba sai an fada musu ba, don haka idan ma cewa aka yi kowa ya kulle kansa, ya kamata mu yi biyayya, shi yasa muke kokarin raba kayan abinci ga jama’a.

“An kulle Masallatan Saudiyya, an kulle birnin Vatican, don haka ina rokon yan Najeriya da sunan Allah su fahimci halin da ake ciki su zauna a gida saboda COVID-19 babu ruwanshi da addininka.” Inji shi.

A wani labari kuma, Hukumar NCDC ta sanar da samun sabbin mutane 5 da suka kamu da annobar Coronavirus a Najeriya, wanda hakan ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 323.

Daily Trust ta ruwaito zuwa yanzu dai cutar ta ratsa jahohi 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja.

“Zuwa karfe 9:10 na daren Lahadi, 12 ga watan Afrilu, akwai mutane 323 da aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 da aka samu rahotonsu a Najeriya, 10 sun mutu, yayin da an sallami 85.” Inji NCDC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel