Rashin tsaro: Mathew Kukah ya soki Shugaba Buhari wajen jana’izar Nnadi

Rashin tsaro: Mathew Kukah ya soki Shugaba Buhari wajen jana’izar Nnadi

Matthew Hassan Kukah, babban Limamin Katolika a Najeriya, ya fito wajen wata jana’iza ya na cewa Najeriya ta shiga gargara a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bishof Matthew Kukah ya yi wannan bayani ne lokacin da aka bizne wani Yaronsu da aka kashe watau Michael Nnadi a Kaduna. Malamin ya soki tafiyar gwamnatin APC mai ci.

“A yau munafunci, yaudara, karyar gaskiya, da nuna mu na kwarai ne da cin amanarmu sun kama mu. Najeriya ta kai gargara, kuma ta na lilo. Wannan kira ne daga gare mu.”

Mathew Hassan ya ke cewa ya kamata ace mutum zai iya mutuwa saboda kishin kasarsa, amma a halin da ake ciki a Najeriya, babu dalilin da zai sa wani ya mutu domin kasar.

Malamin addinin ya soki ‘Yan siyasa wanda ya ce za su iya mutuwa domin su ka kare kujerarsu. ‘"Da zarar mun fara kokarin kai wa ga ci, sai abubuwa su dawo baya daga farko.”

KU KARANTA: Za mu ga bayan 'Yan kungiyar Boko Haram - Sojoji

Rashin tsaro: Mathew Kukah ya soki Shugaba Buhari wajen jana’iza
Rabaren Mathew Kukah ya ce Gwamnatin Buhari ta raba kan jama'a
Asali: UGC

“Me ya ke damun kasar mu ne? ‘Yan Najeriya su tsaya su yi tunani. Babu wanda aka zaba saboda alkawarin da ya yi na kawo karshen Boko Haram irin Muhammadu Buhari.”

“Babu wanda ya taba tunani a ransa cewa nasarar shugaba Buhari za ta kawo mulkin da ake yi yanzu na daga-kai-sai-na-ka, da kuma matsala a harkar tsaro.” Inji Kukah.

Faston bai tsaya nan ba, ya ce: “Babu wanda ya taba tunanin cewa gwamnatin nan za ta kawo tsare-tsaren da za su ka raba kan al’umma da su ke kai kasar daf da kifewa.”

“Wannan shugaban kasar ya nuna matukar ko-in-kula wajen kula da banbance-banbancen Najeriya. Ya yi watsi da bukatan ‘Yan kasa a kan wasu tsirarun mutanensa.”

“Masana, Malamai da Sarakunan Musulunci su na ta faman kukan a kawo addinsu ceto. Saboda Musulunci da Arewa ba su amfana da komai a shekarun gwamnatin nan ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel