Farashin Man Fetur zai Ruguzo a Najeriya bayan Kammala Yakin Iran da Amurka
- An fara fatan ruguzowar farashin man fetur a Najeriya bayan Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki da juna
- Rahotanni sun nuna cewa ana tsammanin matatar Dangote za ta rage farashin litar mai a kwanaki masu zuwa a Najeriya
- Kungiyoyin yan kasuwa sun yi magana kan yadda za a samun sauki a kasuwar mai bayan rikicin Gabas ta Tsakiya ya lafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Farashin fetur na iya sauka har zuwa N900 kan kowace lita a kwanaki masu zuwa idan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin Amurka da Iran ta tabbata kuma farashin ɗanyen mai ya ci gaba da raguwa.
Sababbin abubuwan da suka faru a Gabas ta Tsakiya sun haifar da faɗuwar farashin mai a kasuwannin duniya, lamarin da ya ƙara fatan cewa farashin fetur zai iya raguwa a gidajen mai.

Source: Getty Images
Reuters ta wallafa cewa daga sama da dala 120 kan kowace ganga a watan Afrilun 2026, farashin ɗanyen mai ya ragu zuwa kusan dala 87 kan kowace ganga zuwa ranar Lahadi.
Yadda farashin mai ya tashi a baya
Idan ba a manta ba, ɗanyen mai, wanda shi ne babban sinadarin samar da man fetur, ya tashi daga ƙasa da dala 70 kan kowace ganga bayan rikicin Amurka da Iran ya fara a ranar 28 ga Fabrairun 2026.
A cikin fiye da watanni uku na rikicin, farashin ɗanyen mai ya riƙa kai wa sama da dala 100, har ma ya wuce dala 120 a wasu lokuta, lamarin da ya janyo tashin farashin man fetur a duniya.
Idan muka dawo gida Najeriya, farashin fetur ya tashi daga kusan N830 kan kowace lita zuwa N1,300/
Farashin dizal da man jiragen sama ma sun ƙaru sosai, inda a wani lokaci kamfanonin jiragen sama suka yi gargaɗin cewa hauhawar farashin na iya shafar ayyukansu.
Farashin mai zai ragu a Najeriya
Da yake farashin ɗanyen mai na ci gaba da raguwa a ‘yan kwanakin nan, ana ta hasashen cewa matatar Dangote na iya sake rage farashin fetur domin ya dace da halin da kasuwa ke ciki a yanzu.
A baya, matatar Dangote ta rage farashin fetur daga N1,275 zuwa N1,250 kan kowace lita, yayin da ta rage farashin dizal daga N1,800 zuwa N1,700 kan kowace lita.
Wata majiya daga matatar Dangote ta shaida wa Punch cewa a al’ada ana sa ran za a rage farashin fetur duk da cewa suna da danyen mai da aka saya da tsada.

Source: Getty Images
Majiyar, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce fetur na iya sauka har zuwa N900 kan kowace lita idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da raguwa.
Tun da farko, kungiyar masu gidajen mai ta Najeriya (PETROAN) ta yi hasashen cewa farashin fetur na iya sauka ƙasa da N1,000 kan kowace lita idan aka sake buɗe mashigar ruwan Hormuz.
Da yake magana, sakataren yaɗa labarai na PETROAN, Joseph Obele, ya ce farashin man fetur zai ci gaba da raguwa yayin da farashin ɗanyen mai ke saukowa.
Za a bude mashigar Hormuz
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa Iran za ta bude mashigar Hormuz.
Shugaba Trump ya bayyana haka ne bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran a ranar Lahadi, 14 ga watan Yunin 2026.
Sanarwar da ya fitar ta sanya farashin danyen mai ya yi kasa sosai a kasuwar duniya kuma masana na cewa zai cigaba da sauka.
Asali: Legit.ng


