Kira ga Musulmai: A saurari sanarwar ganin wata daga bakin Sarkin Musulmi kafin daukan azumi

Kira ga Musulmai: A saurari sanarwar ganin wata daga bakin Sarkin Musulmi kafin daukan azumi

Jama’tul Nasril Islam ta yi kira ga kafatanin Musulman Najeriya da su saurari sanarwar mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar kafin su dauki azumin watan Ramadan.

Daily Trust ta ruwaito sakataren JNI, Khalid Aliyu ne ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace Sarkin Musulmi ne kadai ke da hakkin sanar da ganin watan Ramadan.

KU KARANTA: Darajar gangar danyen ta sauka zuwa dala 11 a kasuwannin duniya

Don haka Khalid ya nemi Musulmai su nemi wata, sa’annan su sanar da shuwagabannin addinin Musulunci mafi kusa domin a sanar da Sarkin kafin a sanar ma al’umma.

Mai alfarma Sarkin Musulmai zai sanar da ganin watan bayan gudanar da bincike an tabbatar da sakon da aka aika masa na ganin watan gaskiya ne, daga nan sai ya sanar ma jama’a.

“JNI na kira ga Musulmai su shirya domin ribatan watan azumin Ramadan, wata mai albarka, daga cikin muhimman lamurra na wannan wata akwai batun ganin wata wanda a yan shekarun baya an tsaftace tsarin neman watan da ganinsa.

“Shuwagabannin Musulmai kada su gajiya wajen hada kawunan al’umma Musulmai ta hanyar wayar da kai da kuma ilimantarwa. Kamar yadda aka saba, kada wani ya rudemu game da batun ganin wata, idan ba Sultan ne ya sanar ba.” Inji shi.

Kira ga Musulmai: A saurari sanarwar ganin wata daga bakin Sarkin Musulmi kafin daukan azumi

Kira ga Musulmai: A saurari sanarwar ganin wata daga bakin Sarkin Musulmi kafin daukan azumi
Source: Depositphotos

Haka zalika JNI ta yi kira ga Musulmai su dage da karatun Al-Qur’ani a yayin zaman gida a watan Azumin Ramadan, kada a bari lokacin ya tafi haka nan ba tare an ci moriyarsa ba.

Daga karshe sanarwar ta nemi Musulmai su gudanar da dukkanin ibada na watan Ramadana a gida, har da sallar Tarawihi bisa umarnin gwamnati na kulle masallatai saboda Coronavirus.

Haka zalika ba za’a gudanar da tafsiri a Masallatai ba duk saboda wannan umarni na gwamnati, an yi hakan ne don kare yaduwar cutar annobar Coronavirus a cikin al’umma.

A hannu guda, gwamnatin jahar Borno ta samu nasarar binciko mutane 99 da suka yi mu’amala da mutum na farko da ya kamu da annobar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito wani jami’in kiwon lafiya ne ya fara kamuwa da cutar a jahar, wanda kuma ta yi sanadiyyar mutuwarsa a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel