Sultan ya bada umarnin rufe dukkan masallatan Abuja saboda coronavirus

Sultan ya bada umarnin rufe dukkan masallatan Abuja saboda coronavirus

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa majalisar Musulunci a karkashin jagorancin Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar, ta bayar da umarnin a rufe dukkan masallatan da ke babban birnin tarayya, Abuja.

A bisa ga wata sanarwa daga daraktan majalisar, Yusuf Nwoha, an umurci musulmai da su dunga yin sallar a cikin gidajensu.

Tuni dai dama Kwamitin Babban Masallacin Juma’a na Kasa da ke Abuja, ya bada sanarwar kulle masallacin, domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Sultan ya bada umarnin rufe dukkan masallatan Abuja saboda coronavirus

Sultan ya bada umarnin rufe dukkan masallatan Abuja saboda coronavirus
Source: Depositphotos

Nwoha ya ce an cimma matsayar amincewa a rufe dukkan masallatan Abuja ne bayan an kulla yarjejeniya tsakanin Sultan Sa’ad da kuma manyan malaman Musulunci.

Sanarwar ta yi kira ga dukkan limaman masallatan su bi wannan umarnin da aka bayar na rufe masallatan, har zuwa lokacin da za a bada sanarwar sake bude su.

An kuma yi kira ga al’ummar Musulmi su bai wa gwamnatin tarayya hadin kai domin a gaggauta shawo kan cutar Coronavirus, kada ta yi mummunar barkewa a kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe mutum na farko a Saudiyya

A wani labarin kuma mun ji cewa mugunyar annobar nan mai toshe numfashi watau Coronvirus ta kama babban makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Malam Abba Kyari.

Premium Times ta ruwaito jaridar This Day ne ta fara wallafa labarin Abba Kyari ya kamu da cutar bayan an gudanar da gwaji a kansa da kuma maigidansa, shugaba Buhari, inda sakamakon gwajin ya nuna Buhari bai kamu da cutar ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abba Kyari ya dade a cikin kwamitin gudanarwar jaridar ThisDay, sai dai koda yake an tabbatar da kamuwar tasa, majiyoyin sun shaida a yanzu yana killace a gidansa, kuma baya cikin damuwa.

Majiyar ta shaida cewa Kyari ya kai ziyara kasar Jamus ne a ranar 7 ga watan Maris, inda ya dawo Najeriya bayan kwanaki 7, don haka ake ganin a can kasar ya dauko cutar, sakamakon kasar na fama da yaduwar cutar, wanda har ta kai ga shugaban kasar, Angela Merkel ta killace kanta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel