Ogun
Akalla mutane biyu ne suka samu munana rauni sakamakon barkewar rikicin kabilanci tsakanin yan kabilar Hausa da kabilar Yarbawa dake kasuwanci a kasuwar Lafenwa dake garin Abekuta, babban birnin jahar Ogun.
Mun samu labari cewa Gwamnan Ogun, Mista Dapo Abiodun, ya yi wa ‘Yan APC da su ka jefi Buhari a Kamfe afuwa. Gwamnan ya ce komai ya wuce yanzu.
An shiga cikin tashin hankali da dimuwa yayin da wata mummunan gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo dake garin Abekuta, babban birnin jahar Ogun.
Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Yinka Mafe, ya mutu a daren ranar Talata, jim kadan bayan bikin cikarsa shekara 46.
Mun fahimci cewa babu ruwan ‘Yanuwan Obasanjo da shari’ar da za ayi da shi a kotu. Mutanensa sun kai Obasanjo da Kaninsa da Matarsa kara a kotu kwanan nan.
Rahotanni sun kawo cewa Allah ya yiwa zababben shugaban kwamitin rikon kwarya a yankin karamar hukumar Ipokia da ke jihar Ogun, Saibu Adeosun Mulero rasuwa. Ya rasu ne yan sa’o’i kadan kafin majalisar dokokin jihar ta tantance shi
Kamar yadda Kiristoci ke yada addinin Kirista, kuma a rungumeshi, haka musulmai ke yi ba tare da sassautawa ba. A hakan kuwa kowanne lokaci ake samun wadanda ke sauya addinin da suke bi da farko zuwa wani daban...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana sadaukar da dukkanin nasarorin daya samu a rayuwarsa a lokacin da ya yi shugabanci a karkashin tsarin mulkin Soja da na mulkin dimukradiyya ga Allah Ubangiji.
Saboda harkar tsaro, Gwamnonin Kudu 6 sun kirkiri Jami’an da za su fara aiki a farkon 2020. Gwamnonin sun kafa Jami’ai domin maganin matsalar tsaro kamar yadda mu ka ji Ranar Laraba, 1 ga Watan Junairun 2019.
Ogun
Samu kari