Fadar Shugaban Kasa Ta Firgita da Kalaman Atiku kan 2027, Ta Yi Masa Martani

Fadar Shugaban Kasa Ta Firgita da Kalaman Atiku kan 2027, Ta Yi Masa Martani

  • Fadar shugaban kasa ta yi wa Atiku Abubakar martani game da wasu bayanai da ya yi kan neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa
  • Atiku da yake jigo ne a jam'iyyar ADC ya nuna cewa ba zai sake tsayawa takara ba bayan zaben 2027, lamarin da ke nuna za a fafata da shi
  • Fadar shugaban kasa ta yi masa martani da cewa zai maimaita kuskuren da ya yi a baya, inda ta bukace shi da ya hakura da takara a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hankalin fadar shugaban kasa ya koma kan wasu maganganu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi.

Bayan kammala taron jam'iyyar ADC, Atiku ya sanar da cewa yana shirye ya yi takara a zaben 2027, kuma daga nan ba zai sake takara ba.

Kara karanta wannan

Atiku: "Yadda ADC za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027"

Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a hagu, Atiku Abubakar a gefen dama. Hoto: Bayo Onanuga|Paul O Ibe
Source: Facebook

Mai magana da yawun shugaba Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga ya fusata da kalaman Atiku, inda ya ce akwai kuskure a cikin kalaman Atiku a wani sako da ya fitar a X.

Kiran fadar shugaban kasa ga Atiku

Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa Atiku Abubakar ya dauko hanyar rusa tsarin karba-karba domin mayar da mulki Arewa.

Game da shirin takarar Atiku, Onanuga ya ce:

"Abubakar Atiku ya fito da wata hujja da ta fi karkata ga neman cimma muradinsa, domin kare yunƙurinsa na kawo cikas ga tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu a Najeriya."
"A shekarar 2023, yana cikin jam’iyyar PDP, Atiku ya yi watsi da wannan ka’ida, inda ya nemi ya gaji wani ɗan Arewa da ya shafe shekaru takwas yana mulki.

Magana kan takarar Atiku a ADC

Fadar shugaban kasa ta caccaki Atiku Abubakar kan cewa tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa ba ya cikin kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

"Duk na kere su": Atiku ya kwatanta farin jininsa da na Kwankwaso, Tambuwal a Arewa

Premium Times ta rahoto ta ce:

"Ya nace cewa ba dole ne ya bi wannan tsari ba, yana mai cewa Kudancin ƙasar ne ya fi Arewa yawan shekarun mulki tun daga 1999. Wannan lissafin siyasar nasa cike yake da shakku.
"Ya yi watsi da gaskiyar cewa ƙarancin shekarun mulkin Arewa ya samo asali ne daga rasuwar tsohon Shugaban ƙasa Umaru Yar’Adua kafin wa’adinsa ya cika, lamarin da ya sa Goodluck Jonathan ya gaje shi."

"Dole Tinubu ya yi shekara 8,' Onanuga

Bayo Onanuga ya bayyana cewa tunda Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas, kuma dan Arewa ne, dole Tinubu ma da ya fito daga Kudu ya yi shekaru takwas.

Ya ce:

"Tunda Buhari ya kammala shekaru takwas, dole Tinubu ma ya kammala nasa.
"Abin da ya rage wa Atiku shi ne ya hakura da tunanin sake tsayawa takara, domin har yanzu mulki na hannun 'yan Kudu a zaɓen 2027."
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya yayin wani jawabi a jihar Katsina Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

APC ta ce za ta yi nasara a Kano

Kara karanta wannan

Kwankwaso ko Obi: Atiku ya fadi dan takarar da zai iya goya wa baya a ADC

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya sanar da cewa suna kan hanyar samun nasara.

Ya bayyana haka ne yayin da ya yi hira da manema labarai game da halin da jam'iyyar ke ciki yayin da take karbar masu sauya sheka.

Nentawe ya bayyana cewa APC tana cigaba da samun goyon baya a jihohi kuma masu kada kuri'a a Kano da Kastina na tare da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng