Yansanda sun yi ram da maigadin makabarta ya kwakulo gawar mutum daga cikin kabari

Yansanda sun yi ram da maigadin makabarta ya kwakulo gawar mutum daga cikin kabari

Rundunar Yansandan jahar Legas ta kama wani mutumi dake gadin makabarta da busashshen kan wata gawa daya kwakule kabarinta a wata makabarta dake jahar Ogun, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.com shugaban Yansandan shiyya ta biyu data kunshi jihohin Legas da Ogun, AIG Lawal Shehu ya bayyana cewa Yansanda sun kama mai gadin ne mai suna Jimoh Adeola da kan mutum a ranar Litinin 3 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Boko haram: Buhari ya umarci shugaban hafsoshin sojan sama da ya tare a Borno

“A ranar 3 ga watan Disamba da misalin karfe 8:30 da rabi mun kama wani mutumi mai suna Jimoh Adeola dake gadin makabartar Musulmi dake unguwar Oke Yadi, Abekuta da kan mutum” Inji AIG Lawal.

A cewar AIG Lawal, bincikensu ya bayyana cewa maigadi Adeola ya dade yana kwakulan makabarta yana kwashe gawarwakin jama’a don sayar ma mutane don amfanin dasu wajen yin tsafe tsafe.

“Kwararrun jami’an Yansanda sun gudanar da bincike akan wasu mutane biyar da suka kama dake da hannu cikin satar gawarwakin mutane daga makabartar, suma an kamasu da sassan jikin mutane.” Inji AIG Lawal.

Bugu da kari, AIG Lawal ya bayyana cewa sun kama wasu gagga gaggan yan fashi da makami akan babbar hanyar garin Otta na jahar Ogun, inda yace a yayin da ake gudanar da bincike akansu sun bayyana cewa sun kwace motoci guda biyar, inda zuwa yanzu Yansanda sun kwato guda uku sun mika masusu.

Motocin guda uku sun hada da Toyota Venza, Honda Crosstour da Toyota Highlander, sai dai a cewar AIG Lawal, sauran motocin guda biyu kuma an haura dasu kasar Bini, kuma a can aka sayar dasu.

Daga karshe AIG Lawal yace sun kwato wata babbar mota kirar DAF mai lamba KTG165YG da wasu yan fashi da makami guda biyu da suka sato motar, inda ya kara da cewa suna nan suna bin diddigin sauran yan fashin da suka tsere.

Daga karshe AIG Lawal yace zasu sun gurfanar da dukkanin masu laifin gaban kotun da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel