Abu Ya Masa Daɗi: Tinubu Ya Jefa wa Atiku Magana game da Rikicin ADC
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zargi Atiku Abubakar da yunƙurin jefa jam’iyyar ADC a aljihunsa amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba
- Tinubu na wannan batu ne yayin da rikicin shugabanci na jam'iyyar masu hamayya ta ADC ke kara tsananta sakamakon rabuwar kai
- Tun bayan ƴan haɗakar jam'iyyu sun farfaɗo da ADC ne aka samu tsofaffin ƴan jam'iyya na kalubalantar shugabancin David Mark
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, yana zarginsa da yunƙurin mallakar jam'iyyar hamayya ta ADC.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu na shekarar 2026 yayin da yake karɓar baƙuncin tawagar jakadun shirin “Renewed Hope” a fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Kalaman Atiku sun girgiza fadar shugaban kasa, ta fadi abin da Tinubu zai yi masa a 2027

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubuya danganta rikicin shugabancin jam’iyyar ADC da ƙoƙarin Atiku na mallakar jam’iyyar.
Bola Tinubu ya magantu kan Atiku Abubakar
Lere Olayinka ya wallafa bidiyon Tinubu a shafinsa na Facebook inda Shugaban ya ce Atiku ya taɓa rike mukamin shugaban majalisar kula da sayar da kadarorin gwamnati a Najeriya.
Bola Tinubu ya bayyana cewa amma sakamakon ayyukan nasa bai haifar da wani gagarumin ci gaba ba.
Ya ce:
“Shi shugaban (Atiku) shi ne shugaban majalisar cefanar da kadarori ta ƙasa. Ya sayar da masana’antar ƙarafa a Delta; shin tana aiki a yau? A’a. Ya sayar da Ajaokuta; shin tana aiki a yau? A’a. Zan iya ci gaba da lissafa misalai. Suna ƙoƙarin mallake jam’iyyar wani, amma mai ita ya ce a’a.”
Tinubu ya ƙara da cewa wannan yunƙuri na Atiku shi ne ya haddasa rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar ADC a halin yanzu.
Yadda rikicin ADC ya fara kamari
Tun daga watan Yuli na shekarar 2025, bayan wata haɗakar jam’iyyun adawa ta karɓi shugabancin ADC, jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.
Wani tsohon mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar, Nafiu Bala, ya zargi shugabancin da David Mark ke jagoranta da cewa an naɗa shi ba bisa ƙa’ida ba.

Source: Twitter
A halin yanzu, jam’iyyar ta rabu gida uku, inda ɓangarori ke karkashin jagorancin David Mark, Nafiu Bala, da kuma Ogga Kingsley.
A ranar 1 ga Afrilu, 2026 hukumar INEC ta daina yarda da ɓangaren Mark da kuma na Nafi'u Bala, bayan wani hukuncin wucin gadi da kotun daukaka kara ta yanke.
Haka kuma, kotun koli ta sanya ranar 22 ga Afrilu, 2026 domin sauraron ƙarar da Mark ya ɗaukaka, yana kalubalantar shari’ar da ɓangaren Nafi'u Bala ya shigar dangane da shugabancinsa.
A wani ci gaba, a ranar 13 ga Afrilu, 2026 wani ɓangare na ADC a jihar Adamawa ya dakatar da Atiku Abubakar, yana zarginsa da haddasa rashin haɗin kai a cikin jam’iyyar.
Tinubu ya gana da ƙasashen waje
A baya mun wallafa cewa jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tattaunawa da kasashe domin nemo mafita ga matsalolin tsaro.
Jimoh Ibrahim ya bayyana cewa Najeriya ba ta dogara da kasa guda wajen magance matsalolin tsaro ba, yana mai cewa ana maraba da agaji daga kasashen a Najeriya.
A bayanin da ya yi a Amurka, ya jaddada cewa Najeriya kasa ce mai cikakken iko da za ta ci gaba da zama daya duk da kalubalen da ta ke fama da su a cikin ƙasar.
Asali: Legit.ng

