Gwamnatin tarayya ta fayyace gaskiya game da 'kisan fararen hula' a Borno

Gwamnatin tarayya ta fayyace gaskiya game da 'kisan fararen hula' a Borno

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sojojin sama sun kai hari a kasuwar Jilli bayan binciken sirri kan maboyar ƴan ta'adda
  • Gwamna Babagana Zulum ya tabbatar da cewa an daɗe da rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka gabata saboda ikon da ƴan tada ƙayar baya suke da shi a yankin
  • Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya sanar da cewa an bayar da umarnin gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa kan harin jirgin sojojin sama da aka kai ranar 11 ga Afrilu, 2026, a yankin Jilli da ke ƙaramar hukumar Gubio a jihar Borno.

Gwamnati ta bayyana cewa harin ya fada kan matattarar ƴan ta'adda ne da aka dade ana tattara bayanai game da hada-hadarsu a wurin.

Kara karanta wannan

'Idan na zama shugaban ƙasa," Obi ya faɗi matakin da zai ɗauka kan ƴan bindiga

Gwamnatin tarayya ta fayyace gaskiya game da harin sojoji a kasuwar Jilli
Ministan yada labarai, Mohammed Idris yana jawabi a taron jin bahasi kan ayyukan ministoci. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

Yankin Jilli na hannun ƴan ta'adda

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya fitar a shafinsa na X a yau Talata, 14 ga Afrilu, 2026.

Gwamnati ta jajantawa iyalai da mutanen da harin ya rutsa da su, tana mai jaddada cewa rayuwar kowane ɗan Najeriya tana da daraja.

Sai dai, ta bayyana cewa yankin na Jilli, wanda ake kira "Kasu Daulaye," ya daɗe yana ƙarƙashin ikon ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP, inda suke karɓar haraji da shirya hare-hare.

Dalilan da ya sa aka kai hari Jilli

Sanarwar ta bayyana cewa an kai harin ne bayan kwanaki ana sa ido kan yankin.

Jami'an tsaro sun kafa hujja da kama wani matashi ɗan shekara 15, Tijjani, a ranar 12 ga Afrilu a Ngamdu, wanda ya tabbatar da cewa shi ɗan aiken ISWAP ne dake kai kuɗaɗe da kayayyaki zuwa yankin Jilli.

Kara karanta wannan

Ana barazanar hana ADC taro a Abuja, Atiku ya fadi matakin da za su dauka

Haka kuma, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya tabbatar da cewa hukumance an rufe kasuwar Jilli tun shekaru biyar da suka gabata saboda tana matsayin tungar ƴan ta'adda, in ji rahoton Punch.

Wannan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai wa sojoji ta hanyar binne bama bamai a kan hanyar Jilli da kuma Ngamdu a farkon wannan shekara ta 2026.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta gudanar da cikakken bincike kan harin kasuwar Jilli.
Mutane sun yi dandazo a yankin kasuwar Jilli da ke Yobe inda aka ce sojojin sama sun yi kuskuren kashe 'yan kasuwa fiye da 50. Hoto: @daily_trust/X
Source: UGC

Za a gudanar da bincike don gano gaskiya

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yadda aka tsara da kuma aiwatar da harin domin magance kura-kurai da kuma tabbatar da gaskiya.

Gwamnati tana aiki tare da gwamnatocin jihohin Borno da Yobe, da kuma hukumomin NEMA da SEMA domin tallafa wa iyalai da harin ya shafa.

A gefe guda, Ministan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su kasance masu taka tsantsan wajen bayar da rahotanni kan tsaron ƙasa.

Sojoji sun yi kuskure a harin da suka kai Jalli

Tun da fari, mun ruwaito cewa, jirgin yaƙin sojojin saman Najeriya ya saki wuta a kasuwar mako-mako ta Jilli da ke Yobe inda akalla mutane 200 suka riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

Jiragen yaƙin suna bin sawun ƴan ta'adda ne da suka zo karɓar haraji, sai dai an samu kuskure, inda harin ya faɗa kan talakawa ƴan kasuwa.

Shugabannin yankin sun tabbatar da cewa an kwantar da mutanse da dama a asibitin ƙwararru na Geidam, wasu kuma an tura su Damaturu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com