Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Daliban da Suka Je Yin Jarabawar JAMB

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Daliban da Suka Je Yin Jarabawar JAMB

  • Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai a hanyar zuwa zana jarabawar JAMB, lamarin da ya jefa iyaye da 'yan uwansu a cikin tashin hankali
  • Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tabbatar da cewa jami'an rundunar suna cikin daji domin ceto daliban da aka sace a hanyar zuwa zana jarabawar
  • Mazauna yankin sun nuna matukar damuwa kan yadda wannan hanyar ta zama matattarar ’yan bindiga masu addabar matafiya da sace dalibai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Benue – Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da fasinjoji da dama, ciki har da daliban da ke shirin zana jarabawar shiga jami'a (JAMB), a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo a jihar Benue.

Lamarin ya afku ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Laraba, lokacin da maharan suka tare wata motar bas ta kamfanin Benue Links.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

'Yan bindiga sun sace dalibai a hanyar zuwa zana jarabawar JAMB.
Daliban makarantar sakandaren gwamnati a wajen makarantar lokacin da malamai suka shiga yajin aiki a Abuja a Yunin 2024. Hoto: KOLA SULAIMON/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

'Yan bindiga sun sace masu zana JAMB

Majiyoyi sun bayyana cewa motar na ɗauke da fasinjoji kusan 18, inda mafi yawancinsu matasa ne da ke kan hanyar zuwa Otukpo domin zana jarabawar JAMB da aka shirya gudanarwa a yau Alhamis, in ji rahoton Punch.

Direban motar da wani fasinja ɗaya ne kawai suka samu nasarar tserewa yayin da maharan suka yi awon gaba da sauran fasinjojin zuwa cikin daji.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda girman lamarin, ta bayyana cewa:

“Mutane biyu, direba da fasinja daya ne kawai suka samu nasarar tserewa. Mafi yawan wadanda aka sace matasa ne maza da mata da ke kan hanyar zuwa zana jarabawar JAMB da aka shirya gudanar wa a yau (Alhamis.)

Martanin rundunar ’yan sandan Benue

Kwamishinan ’yan sandan jihar Benue, Ifeanyi Emenari, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026, in ji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce rufin asirin jama'a na cikin nasarar APC a 2027

Ya bayyana cewa fasinjoji 14 ne aka yi garkuwa da su, kuma ya riga ya isa Otukpo domin jagorantar aikin ceto daliban.

Kwamishinan ya bayyana cewa rundunarsa tana binciken dalilin da ya sa direban ya yi tafiyar dare, duba da cewa kamfanin Benue Links yana da dokar hana tafiya bayan awannin aiki sun ƙare.

Emenari ya jaddada cewa:

"Mun riga mun isa garin domin tabbatar da cewa an ceto waɗannan mutane cikin ƙoshin lafiya. Jami'anmu sun riga sun shiga daji domin bin sawun maharan."
Rundunar 'yan sanda ta fara farautar 'yan bindigar don ceto daliban da aka sace.
Taswirar jihar Benue, inda 'yan bindiga suka sace dalibai a hanyar zana jarabawar JAMB. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Damuwar shugabannin yankin kan tsaro

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da cewa an tura jami'an tsaro daban-daban zuwa cikin kurmi domin taimakawa wajen ceto waɗanda aka sace.

Ya nuna matuƙar damuwa kan yadda abin ya shafi matasa ɗalibai waɗanda ke neman ilimi domin gina makomarsu, yana mai cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin ganin sun dawo gida.

Hanyar Makurdi zuwa Otukpo dai ta zama filin daga a watannin baya-bayan nan sakamakon yawaitar hare-haren ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Jagoran 'yan bindiga ya tura sako ga gwamnati, ya fadi matsayar sulhun da aka yi a Katsina

'Yan bindiga sun farmaki Benue Links

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun harbi fasinjoji uku dake tafiya a cikin motar kamfanin Benue Links kusa da garin Otukpo a tsakiyar dare.

Babban manajan kamfanin sufurin ya tabbatar da cewa fasinjojin suna karbar magani sannan kamfanin zai biya dukkan kudaden asibitin.

Hukumar sufurin ta sake jaddada dokar hana tafiyar dare ga dukkan direbobinta domin kaucewa fadawa tarkon yan bindiga a hanyoyin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com