Hatsarin mota ya kashe sabuwar amarya da mutane 4 a jihar Ogun
Mutane biyar da suka hadar da wata sabuwar amarya sun yi gamo da ajali yayin da kimanin mutane 14 suka jikkata a wani mummunar hatsarin mota da ya auku a kauyen Akila dake babbar hanyar Abeokuta zuwa Ibadan ta jihar Ogun.
Cikin mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sun da wata sabuwar amarya tare da angonta a wannan mummunan hatsari da ya auku a tsakanin motoci biyu da misalin karfe 9.20 na daren ranar Juma'ar da ta gabata cikin karamar hukumar Odede ta jihar Ogun.
Kwamandan hukumar kula da lafiyar manyan hanyoyi reshen jihar Ogun, Mista Clement Oladele tare da kakakin hukumar Babatunde Akinyibi, sun bayar da tabbacin aukuwar wannan mummunan tsautsayi da baya wuce ranarsa.
A sanarwar da Akibiyi ya gabatar, hatsarin ya auku yayin da wata babbar motar dakon kaya mai lambar LAR 114 YD ta gwabzawa wata karamar motar haya mai lambar MUS 367 XV a sanadiyar ganganci da kuma tsala gudu na fitar hankali da ya wuce misali.
KARANTA KUMA: 'Yan daban daji sun salwantar da rayuka 10, sun raunata mutane 5 a jihar Katsina
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Akinbiyi ya ce mutane 15 ne da hatsarin ya ritsa da su sun hadar Maza 11 da kuma Mata 4.
Daga bangaren Oladele kuma, hatsarin da ya ritsa da kimanin mutane 19 ya yi sanadiyar salwantar rayuwar mutane biyar nan take yayin da kuma mutane 14 suka jikkata. A halin yanzu su na ci gaba da samun kulawa a cibiyar lafiya ta FMC dake birnin Abeokuta.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng