Ta Faru Ta Kare, Gwamnan Nasarawa Ya Nuna Wanda Zai Gaji Kujerarsa a Zaben 2027

Ta Faru Ta Kare, Gwamnan Nasarawa Ya Nuna Wanda Zai Gaji Kujerarsa a Zaben 2027

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ayyana Sanata Ahmed Wadada a matsayin wanda yake so ya gaje shi a babban zaɓen shekarar 2027
  • Hukuncin gwamnan ya biyo bayan tattaunawa ta tsawon shekara guda da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da sarakuna da kuma ƙungiyoyin matasa
  • Gwamna Sule ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatin sa da su ajiye buƙatun kan su domin mara wa Sanata Wadada baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Nasarawa – Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya fito fili ya nuna wanda yake so ya gaji kujerarsa a zaben 2027 da ke tafe.

Abdullahi Sule ya ayyana Sanata Ahmed Aliyu Wadada, mai wakiltar shiyyar Nasarawa ta Yamma, a matsayin ɗan takarar da yake goyon baya domin ya gaje shi.

Kara karanta wannan

Za a samu barkewar cututtuka a Kaduna, Kogi da jihohi 8, gwamnati ta yi bayani

Gwamnan Nasarawa ya ayyana Sanata Ahmed Wadada a matsayin wanda zai gaje shi a 2027
Sanata Ahmed Aliyu Wadada, mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Yamma. Hoto: Senator Ahmed Wadada.
Source: Facebook

Gwamnan Nasarawa ya zabi magajinsa

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026, a wata ganawa da ya yi da masu riƙe da muƙaman siyasa da shugabannin hukumomin gwamnati a Lafia, in ji rahoton Punch.

Mai girma Abdullahi Sule ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan tattaunawa ta tsawon shekara guda da aka gudanar da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen jihar.

Ya jaddada cewa an bi matakai daban-daban kafin a tsame Sanata Wadada daga cikin mutane uku da aka tantance a matakin ƙarshe na wannan bincike.

A cewar Gwamna Sule, babban abin da aka duba wajen zaben Sanata Wadada shi ne ƙarfinsa wajen iya cin zaɓe da kuma gogewarsa a shugabanci.

Dalilin Gwamna Sule na zaɓar Sanata Wadada

Abdullahi Sule ya bayyana cewa an tuntuɓi sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin matasa, da matan jihar kafin a cimma matsaya ɗaya ta zabar magajinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan neman dawo da tallafin man fetur

Gwamnan ya ƙara da cewa:

"Muna buƙatar mutumin da yake da ƙarfin da zai iya samun nasara a wannan zaɓe, kuma bayan dogon nazari, Sanata Wadada ne ya zama zaɓinmu."

Haka kuma, ya bayyana cewa ƴan takara daga shiyyar Nasarawa ta Yamma sun amince su mara wa duk wanda aka ayyana a matsayin magajin, in ji rahoton Vanguard.

Gwamnan ya buƙaci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da su ajiye buƙatun kan su su koma bayan Sanata Wadada domin tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Gwamna Abdullahi Sule ya bukaci dukkan masu rike da mukamai a Nasarawa su goyi bayan Sanata Ahmed Wadada a 2027.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya na jawabi a wani taro a Lafia. Hoto: @NasarawaGovt
Source: Twitter

Gargaɗi kan cin mutuncin sauran 'yan takara

Duk da cewa ya bayyana wanda yake so, Gwamna Abdullahi ya gargaɗi magoya bayan sa da kada su rinka cin mutunci ko hantarar sauran ƴan takarar da ba a zaɓa ba.

Ya jaddada cewa dukkan waɗanda aka tantance mutane ne masu kima da za su iya jagorancin jihar, kuma zaɓin Sanata Wadada ba yana nufin ya fi kowa ba ne, illa dai wani tsari ne na siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce rufin asirin jama'a na cikin nasarar APC a 2027

Gwamnan ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a jihar Nasarawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gwamna Sule ya nada sabon sarki

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abdullahi Sule ya amince da nadin sabon Sarkin Udege da ke karamar hukumar Nasarawa (Osu Ajiri na Udege).

Gwamna Sule ya nada Alhaji Suleiman Ahmed-Eko a matsayin sabon Osu Ajiri na masarautar Udege da ke ƙaramar hukumar Nasarawa, kuma matakin zai fara aiki nan take.

Gwamnatin Nasarawa ta sanar da wannan nadi ne ta hannun kwamishinar kananan hukumomi, harkokin masarautu da ci gaban al'umma, Alhaja Amina Mu’azu-Maifata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com