Asiri ya tonu: An cafke wasu samari guda uku da suka yiwa wasu tsofaffin ma'aurata gunduwa-gunduwa da adda

Asiri ya tonu: An cafke wasu samari guda uku da suka yiwa wasu tsofaffin ma'aurata gunduwa-gunduwa da adda

- An cafke wasu mutane guda uku a jihar Ogun da laifin yiwa wasu ma'aurata gunduwa-gunduwa da adda

- Bayan gabatar da bincike mutanen sun bayyana cewa su barayi ne, kuma sunje gidan da niyyar sata ne, kawai sai suka fuskanci ma'auratan sun gane daya daga cikinsu

- Wannan dalilin ne yasa suka yi musu gunduwa-gunduwa suka gudu saboda tsoron kada asirinsu ya tonu

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar cafke wasu samari guda uku da ake zargin sun kashe wasu tsofaffin ma'aurata a karamar hukumar Sagamu, dake jihar.

Wani dattijo mai shekaru 72 mai suna James Olaosebikan da matarsa Esther Olaosebikan mai shekaru 68, an bayar da rahoton kisan su a ranar 30 ga watan Yuni a gidansu dake kusa da babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Wakilin Aminiya ya samu rahoton cewa dan gidan mamatan mai suna Joseph Olaosebikan shine ya kai rahoton cewa 'yan ta'addar sun shiga gidan nasu daga sama ne, inda suka yi gunduwa-gunduwa da iyayen nasa.

Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya bayyanawa manema labarai a garin Abeokuta ranar Larabar nan, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Bashir Makama, ya bai wa DPO na ofishin 'yan sanda na Sagamu da yayi gaggawar fito da masu laifin.

KU KARANTA: An gudu ba a tsira ba: Saudiyya ta sake gayyato Janet Jackson da 50 Cent su cashe yau a kasar bayan Nicki Minaj taki zuwa

Ya ce DPO da 'yan sandan sun gabatar da wannan bincike, inda kuma suka gano wadannan masu laifi ta hanyar kama su.

Masu laifin sun hada da, Ibrahim Uthman, Aba Abdulkareem da kuma Abdulhamid Ibraahim.

"Da aka bincike su sun bayyana cewa su 'yan fashi da makami ne, kuma wani dan uwansu ne wanda ya tsere ya gayyace su wannan yanki domin suje su yiwa wadannan mutane fashi.

"Amma suna zuwa gidan sai suka gane mamatan sun gane daya daga cikinsu, hakan yasa suka kashe su," in ji Oyeyemi.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa kwamishinan ya bukaci hukumar binciken manyan laifuka su karbi wannan lamari domin cigaba da bincike akan masu laifin.

Sannan ya bukaci jami'an 'yan sandan su nemo sauran mutun dayan da ya gudu cikin gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng