An Fara Hararo Sallar Layya, Sarkin Musulmi Ya Ce a Fita Duba Watan Zulki’ida
- Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi da ke jihar Sokoto ta fitar da sanarwa game da duba jinjirin watan Zulki’ida a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilun 2026
- Sanarwar ta bukaci dukkan al'ummar Musulmi su fita da yammacin ranar Juma'a, 17 ga watan Afrilun 2026 domin duba watan da sanar da hukumomi
- Wani masanin taurari a Najeriya, Adamu Ya’u Dan America ya yi karin haske game da yadda watan zai fito da batun ganin shi ko akasin haka a Saudiyya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - A jiya Alhamis 16 ga watan Afrilu, 2026, mai alfarma Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa game da fita duba watan 11 a kalandar Musulunci, wato Zulki’ida.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da watan Shawwal ke bankwana, inda ya cika kwana 29 a yau Juma'a 17 ga watan Afrilun 2026.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da fadar Sarkin Musulmi ta fitar a Facebook a wata takarda da Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanyawa hannu.
Za a fita duba watan Zulki’ida
Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta bukaci al'umma su fita duba watan Zulki’ida a yau Juma'a tare da bukatar su sanar da hukumomi.
Sanarwar da ta fitar ta ce:
"Ana sanar da daukacin al’ummar Musulmi cewa ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026, wadda ta yi daidai da ranar 29 ga watan Shawwal 1447AH, ita ce ranar da za a fara duban jinjirin watan Zulki’ida 1447AH."
"Don haka ana rokon Musulmi da su fara duban jinjirin watan Zulki’ida 1447AH a ranar Juma’a, sannan su kai rahoton ganin jinjirin ga hakimi ko shugaban kauyensu mafi kusa, domin a mika ga mai alfarma, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar."
"Allah (SWT) Ya taimake mu wajen sauke wannan nauyi na addini, amin."
Batun ganin wata a Saudiyya a yau
Bayan sanarwar Sarkin Musulmi, masani mai sharhi kan abubuwan da suka shafi taurari, Adamu Ya'u Dan America ya wallafa a Facebook cewa a yau za a ga wata a Saudiyya.
Ya ce:
"Ranar Juma’a 17/04/2026, bayan sallar Magariba, za a samu labarin cewa kasar Saudiyya ta kunna koren haske a saman agogon Ka’aba, wanda hakan ke nuna cewa an ga watan Zulki’ida 1447AH.
"Hakan zai faru ne saboda a ranar Juma’a da misalin karfe 2:51 na rana agogon Saudiyya za a samu haduwar wata da duniya da rana, wanda shi ne asalin samuwar jinjirin wata.
"Haske zai fara bayyana a jikin jinjirin bayan faduwar rana a kasar Saudiyya."

Source: Facebook
Ya kara da cewa Wannan na nufin cewa ranar Asabar 18/04/2026 za ta kasance ranar 1 ga watan Dhul-Qa’ada 1447AH a kasar Saudiyya bisa hasashen da ya yi.
Malami ya sabawa sanarwar Sarkin Musulmi
A wani labarin, mun kawo muku cewa wani malami a jihar Sokoto, Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya sabawa umarnin Sarkin Musulmi yayin sallar azumi.
Malamin ya fita sallar Idi tare da mutanensa a Sokoto duk da cewa fadar Sarkin Musulmi ta sanar da cewa za a yi azumi 30 saboda rashin ganin wata.
Cikin dalilan da ya kawo, Sheikh Lukuwa ya sanar da cewa sun samu labarin ganin wata a kasar Nijar saboda haka wannan ya wadatar da su.
Asali: Legit.ng


