Allah ya kyauta: Bokan mu ne yace mu yanko masa kayuwan 'yan uwanmu zai bamu maganin samun kudi - Masu laifi

Allah ya kyauta: Bokan mu ne yace mu yanko masa kayuwan 'yan uwanmu zai bamu maganin samun kudi - Masu laifi

Wasu yan asiri uku da aka kama sun fada ma rundunar yan sanda cewa bokansu ne ya bukaci da su kawo masa kawunan mutane uku da suka sani domin yayi masu maganin kudi.

Rundunar IRT ne suka kama Sunday Mathew mai shekara 52, Samuel Olaniyi mai shekara 65 da Uchenna Olewunne mai shekara 49, dauke da kan mutum a ranar 6 ga watan Yuli, a Iju kusa da Ota, jihar Ogun.

Sun yi ikirarin cewa bokansu ya fada masu cewa ya zama dole su san sunan duk mutumin da za su yi amfani da kanshi, da kuma sunan wasu daga cikin yan uwansa,da dai sauran bayanai.

Sun biya bokan kudi naira 45,000 wanda yayi amfani dashi wajen hada masu surkulle tare da kan mutumin.

Majiyoyi sun bayyana cewa sun bayar da snuyane sauran mambobin kungiyarsu yayinda suke amsa tambayoyi.

An tattaro cewa masu laifin sun dauki jami’an yan sanda zuwa wajen iyalan daya daga cikin mutanen da suka yi amfani dashi a ranar 9 ga watan Yuli.

Yan uwan marigayin sun bayyana sunansa a matsayin Idowu Jimoh, wanda ya rasu yana da shekara 19 a ranar 15 ga watan Nuwamba , 2018 biyo bayan yar gajeriyar rashin lafiya sannan aka binne shi a gidan iyayensa.

Daya daga cikin masu lain, Samuel Olaniyi, ya kasance dan uwan Idowu Jimoh.

KU KARANTA KUMA: Abunda Buhari ya fada ma shugabannin majalisar dokoki kan sunayen ministoci - Kalu

Mathew wanda yayi ikirarin cewa shi manoni ne daga Ipokia, jihar Ogun yace wannan ne karo na farko da yayi amfani da mutum don yin asiri.

Uchenna, bokan, ya karyata batun kasancewa mai yin kudin asiri. Yayi ikirarin cewa shi kwararre ne kawai a harkar warkar da cuttutuka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel