Riko da addini ya sa na gina Masallaci da Coci a dakin karatu na - Obasanjo
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana dalilin da ya sanya ya gina wuraren ibada na manyan addinai biyu a kasar na Islama da Kirista a harabar dakin karatunsa dake birnin Abeokuta.
Obasanjo kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ya ce riko da addini da kuma bukatar cikar alkawali ya sanya ya yanke shawarar gina coci da masallaci a harabar dakin karatunsa mai sunan Olusegun Obasanjo Presidential Library dake mahaifarsa ta jihar Ogun.
Obasanjo a ranar Litinin cikin birnin Abeokuta, ya bayyana hakan a wata sanarwa da sa hannun mai magana da yawunsa, Kehinde Akinyemi.
A sanarwar da hadimin tsohon shugaban kasar ya fitar, wadanda ba sa goyon bayan samuwar wuraren ibada a dakin karatun na ci gaba shan kunya duba da yadda wuraren ibadar ke ci gaba samun tabarraki da bunkasa ta fuskar yadda mutane ke tururuwa a cikin su.
Ana iya tuna cewa tsohon shugaban Najeriya Obasanjo, ya sha suka ta manyan kasar nan musamman jigon kungiyar dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai, biyo bayan wasikar da ya rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Yulin da ya gabata.
KARANTA KUMA: Zaben 2019 alama ce ta bunkasar dimokuradiyya a Najeriya - Buhari
Wasikar, wacce Obasanjo ya aika a ranar 15 ga watan Yulin 2019, ta kunshi sakonnin gargadi ga shugaba Buhari musamman kan al'amuran tsaro inda har ya ce yaki na daf da barke wa a Najeriya idan Buhari bai sauya halinsa na ko in kula ba.
Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, tsohon shugaban na Najeriya ya ce matsalar tsaro a kasar na iya janyo a kai wa Fulani harin ramuwar gayya, lamarin da ka iya jefa kasar cikin tarzoma ta kisan-kare-dangi irin wanda kasar Rwanda ta fuskanta a baya.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng