APC ta ruguza duka shugabannin ta a Jihohin Imo da Ogun

APC ta ruguza duka shugabannin ta a Jihohin Imo da Ogun

- APC ta rugurguza daukacin shugabannin ta a Jihohin Imo da Ogun

- Jam'iyyar ta dauki wannan mataki ne a wani zama da aka yi jiya

- Gwamna Okorocha da Amosun na neman ba APC ciwon kai a 2019

APC ta ruguza duka shugabannin ta a Jihohin Imo da Ogun

APC NWC ta rusa shugabannin ta a Jihohin Imo da Ogun
Source: UGC

Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa rikicin cikin gidan da yake kunno kai a Jam’iyyar APC mai mulki ya sa Uwar Jam’iyyar ta rusa shugabannin ta da ke Jihohi na Imo da kuma Ogun domin gudun samun matsala a zaben 2019.

Jam’iyyar APC ta tsige gaba daya shugabannin ta na Jihar Imo da kuma Jihar Ogun. Haka zalika kuma an ruguza shugabannin APC na kananan hukumomi da duk gundumomin Jihohin 2. A jiya ne dai wannan labari ya shiga gari.

Uwar Jam’iyyar za ta nada shugabannin rikon kwarya a halin yanzu a wadannan wurare kamar yadda mu ka samu labari. Shugaban Jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole da kuma Majalisar sa ta NWC ne su ka dauki wannan mataki.

KU KARANTA: Ana kokarin tsige Bukola Saraki daga kujerar sa - PDP

Adams Oshiomhole wanda shi ne Shugaban APC ya bayyana cewa Jam’iyyar za tayi cikakken bayani game da wannan mataki da aka dauka ta bakin Mallam Lanre Issa-Onilu. Onilu shi ne Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC.

Majiyar mu ta tabbatar mana cewa APC ta dauki wannan mataki ne a dalilin sauya-sheka da manyan mukarabban Gwamnonin Jihohin Imo da Ogun su ke yi zuwa wasu Jam’iyyun hamayya, wanda hakan na iya ba APC cikas a 2019.

A Jihar Imo dai Rochas Okorocha ya sha alwashin ganin Surukin sa ya doke ‘Dan takaran APC a zaben Gwamna da za ayi. Haka kuma a Jihar Ogun, na-kusa Gwamna Ibekunle Amosun sun fice daga Jam’iyyar sun koma wata Jam’iyya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel