An daure dan Fulani biyo bayan mummunar barnar da shanunsa suka tafka a gonar manomi
Rundunar Yansandan jahar Ogun ta tasa keyar wani bahillaci mai shekaru 40 a rayuwa, Abubakar Usman gaban wata kotun Majistri dake garin Abekuta sakamakon mummunar barna da shanunsa suka tafka a gonar wani manomi a jahar.
Majiyar Legit.com ta ruwaito shanun bahillace Usman sun barnata amfanin gona da darajarsu ta kai naira miliyan hudu (N4,000,000) a wata gona dake kauyen Alagbagba a garin Abekuta na jahar Ogun.
KU KARANTA: An yanka ta tashi: Shuwagabannin Inyamurai sun yi fatali da takarar Atiku Abubakar
Dansanda mai shigar da kara, Inspekta Olubisi Lawrence ya shaida ma kotu cewa wanda ake zargi ya tura dabbobinsu cikin gonar da ake magana akai ne a ranar 10 ga watan Oktobar shekarar 2018 da misalin karfe 5 na yammacin ranar.
Inspekta Lawrence yace Usman da sauran abokansa da a yanzu sun cika wandunansu da iska sun hada baki suka kada dabbobinsu cikin gona mallakin Segun Oyeku, gonar dake cike da masara da ganyayyaki da suka kai na naira miliyan 4.
Don haka yace suna tuhumar Usman da aikata laifuka uku, hadin baki wajen aikata laifi, shiga gonar da tasu ba da kuma barnata dukiya, wanda yace laifukan sun saba ma sashi na 517, 81 da 451 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Ogun.
Sai dai wanda ake kara ya musanta aikata laifukan duka, don haka Alkalin kotun, Olarewaju Onagoruwa ta bada belinsa akan kudi naira dubu dari biyu (N200,000) da mutane biyu da zasu tsaya masa akan dubu dari bibbiyu suma.
Daga karshe Alkali Onagoruwa ta tasa keyar Usman zuwa gidan yari har sai ya cika sharuddan beli, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Janairun shekarar 2019.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng