Isra'ila Ta Karya Yarjejeniya a Lebanon, Ta Kai Munanan Hare Hare bayan Jawabin Trump

Isra'ila Ta Karya Yarjejeniya a Lebanon, Ta Kai Munanan Hare Hare bayan Jawabin Trump

  • Rahotanni sun ce ana ci gaba da harbe-harbe da kai hare-hare wasu sassan kasar Lebanon duk da bayanin shugaban Amurka
  • Shugaba Donald Trump ya bayar da tabbacin cewa Isra'ila za ta dakata da kai hare-hare zuwa Lebanon a wani bangare na yin sulhu
  • Amma sojojin Isra’ila na amfani da manyan bindigu da jiragen leƙen asiri a yankunan kudancin Lebanon da Bekaa Valley

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Israel – Duk da cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki ƙasa da awa guda da ta wuce, rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da hare-hare a wasu yankuna na Lebanon.

A gano sojojin Isra’ila sun ci gaba da harba manyan bindigu kan garuruwan Khiam da Dibbine da ke kudancin Lebanon bayan fatali da tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Lebanon ta watsa wa Trump kasa a ido, ta dauki mataki na ban mamaki kan Isra'ila

Isra'ila ta ci gaba da kai hari Lebanon
Wani makami mai linzami kirar Fateh 110 da aka harba a yakin Gabas ta Tsakiya Hoto: Mohsen Shandiz/Corbis via Getty Images Source: Getty Images
Source: Facebook

Al-Jazeera ta wallafa cewa rahoton ya ce harbe-harben ba su tsaya nan ba, domin ana kuma gudanar da farmaki da amfani da bindigu masu saurin harbi a kan jama'a a yankunan.

Isra'ila ta yi watsi da tsagaita wuta

The Times ta wallafa cewa wannan yanayi na nuna cewa tsagaita wutar da aka sanar bai samu cikakken aiwatar wa ba daga ɓangaren Isra'ila ba.

A cewar rahotanni, wadannan hare-hare sun jefa al’ummar yankunan cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da sa ido kan yadda lamarin ke tafiya bayan sanar da tsagaita wutar.

A wani bangare kuma, rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da zirga-zirgar jiragen leƙen asirin Isra’ila a yankin yammacin Bekaa Valley.

Jiragen Isra'ila na shawagi a Lebanon

Haka kuma an ga jiragen na shawagi a sararin samaniyar yankin Rashaya da kuma gangaren yammacin tsaunin Jabal al-Sheikh, inda suke gudanar da ayyukan sa ido mai tsanani.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

Sojojin Isra'ila na harba bindigu da a cikin Lebanon
Firaministan ƙasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Getty Images

Wannan nuna cewa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, ana ci gaba da ayyukan soja a wasu yankuna, abin da ke kara tayar da hankalin jama’a da kuma jefa shakku kan dorewar zaman lafiya a yankin.

Ana ganin irin wadannan rahotanni na iya kawo cikas ga kokarin tabbatar da zaman lafiya, musamman idan bangarorin da ke rikici ba su mutunta yarjejeniyar da aka cimma ba.

Ana sa ran cewa hukumomi da masu ruwa da tsaki za su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an mutunta tsagaita wutar, tare da dakile duk wani sabon tashin hankali a yankin.

An sanar da tsagaita wuta a Lebanon

A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen Israila da Lebanon.

Donald Trump ya bayyana cewa ya yi magana da shugabannin kasashen biyu domin ganin an samu zaman lafiya bayan an kai ruwa rana kan tsagaita wuta.

Shugaban na Amurka ya yi alfahari da cewa ya magance yakoki tara a fadin duniya kuma wannan tsagaita wutar ta zama ta 10 duk da harin da ƙasarsa ke kai wa Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng