"Ba Mu Yarda ba," Malaman Musulunci Sun Tunkari Gwamna kan 'Tsarin' da Ya Kawo a Najeriya

"Ba Mu Yarda ba," Malaman Musulunci Sun Tunkari Gwamna kan 'Tsarin' da Ya Kawo a Najeriya

  • Malaman addinin musulunci sun taso Gwamna Dapo Abiodun bayan ya yi yunkurin maida makarantun kiristoci hannun masu su na asali
  • Kungiyar limamai da malaman musulunci ta jihar Ogun ta ce hakan rashin adalci ne kuma musulmai ba za su yarda da wannan mataki ba
  • Sun bukaci gwamnan ya gaggauta canza shawara matukar yana son tabbatar da adalci da daidaito tsakanin al'ummar da ta kunshi addinai daban-daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Kungiyar Limamai da Malamai na Addinin Musulunci a Jihar Ogun ta yi watsi da shirin Gwamna Dapo Abiodun na mayar da makarantun mishan, "Missionary Schools," da ke hannun gwamnati ga kiristoci.

A makon da ya gabata ne gwamnan Ogun ya bayyana aniyarsa ta mayar da wadanna makarantu ga masu su na asali, a matsayin wani bangare na kokarin karfafa hadin gwiwa a fannin ilimi.

Kara karanta wannan

Amurka ta toshe Hormuz, Kim Jong Un ya harba makamai masu iya harbo jirage

Gwamna Aboidun.
Gwamnan jihar Osun, Prince Dapo Abiodun da wurin taro Hoto: Prince Dapo Abiodun
Source: Twitter

Shirin Gwanna Aboidun na maida makarantu

Daily Trust ta ce Abiodun ya fadi hakan ne ranar Juma’a yayin da ya karbi bakuncin jakadan Vatican a Najeriya, Archbishop Michael Francis Crotty, a ofishinsa da ke Oke-Mosan a Abeokuta, tare da wasu manyan limaman cocin Katolika.

Ya ce gwamnatinsa na da niyyar mayar da dukkan makarantun ga masu su, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu da kuma coci-coci domin bunkasa ci gaba.

Sai dai a wata sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar Limamai da malaman addinin musulunci a Ogun Imam Tajudeen Mustafa Adewunmi, ya fitar, ya ce ba su amince da wannan tsari ba.

Musulmai sun yi fatali da shirin Abiodun

Malaman sun bayyana rashin amincewarta da wannan shiri, suna mai cewa hakan ya sabawa daidaito da adalci a cikin al’umma mai addinai daban-daban.

Kungiyar malaman musuluncin ta ce an karbe wadannan makarantu a baya ne domin kawar da bambancin addini a harkar ilimi, don haka mayar da su yanzu zai iya jawo sabani da rashin jituwa a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

Malamin addinin Musulunci ya shiga takarar gwamnan Zamfara, ya zabi jam'iyya

A cewar Tajudeen Adewunmi, dawo da irin wannan tsari zai iya haifar da rabuwar kai, karfafa rashin yarda da juna, tare da lalata zaman lafiya da aka dade ana morewa a jihar.

Matsalar da malamai suka hango

Shehin ya ce matakin na nuna wariya kuma ba za a amince da shi ba, yana mai zargin cewa gwamnati na kokarin fifita wata kungiya ta addini a kan sauran al’umma, kamar yadda Punch ta kawo.

Kungiyar ta kuma gargadi cewa al’ummar Musulmi, wacce ke da gagarumar rawa a jihar, ba za ta zauna shiru ba idan aka ci gaba da watsi da hakkokinta da gudunmawarta.

Jihar Ogun.
Taswirar jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta bukaci gwamnati da ta yi watsi da wannan shiri gaba daya ba tare da wani sharadi ba, tana mai cewa:

"Duk wani mataki da ba wannan za mu dauke shi a matsayin rashin adalci da nuna wariya," in ji kungiyar.

Gwamnan Ogun ya ji dadin ziyarar Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya yi godiya ga shugaban kasa, Bola Tinubu, bisa ziyarar da ya kai jihar domin kaddamar da manyan ayyuka.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad

Abiodun ya bukaci shugaban kasar da ya ci gaba da yaki da aikata laifuffuka a kasar da kuma ta'addanci da ake fama da shi.

Gwamnan ya tabbatar da cikakken goyon bayan al'ummar Ogun ga shugabancin Tinubu inda ya ce yan jiharsa suna tare da shugaban kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262