Mutane uku sun mutu yayin da masu garkuwa da mutane suka yi yunkurin kubutar da abokansu da aka kama

Mutane uku sun mutu yayin da masu garkuwa da mutane suka yi yunkurin kubutar da abokansu da aka kama

Biyu daga cikin wasu mutane hudu da aka kama bisa zarginsu da garkuwa da mutane tare da wani abokinsu guda daya sun rasa ransu yayin musayar wuta da jami'an 'yan sanda.

An yi musayar wutar ne yayin da jami'an 'yan sanda suka debi masu laifin da suka kama daga Ijebu zuwa hedikwatarsu da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Abokan masu garkuwa da mutanen sun yi kwanton bauna a hanya tare da bude wa motar jami'an tsaro wuta a tsakanin J4 da Abigi domin su kubutar da abokansu.

An kama masu garkuwa da mutanen ne bayan sun fito daga cikin surkukin da suka buya bayan sun kama wani dan babban limami a ranar Sallah.

A ranar 16 ga watan Agusta ne jami'an 'yan sanda suka samu nasarar kubutar da mutumin da aka sace tare da kama daya daga cikin masu garkuwa da mutanen.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, jami'an 'yan sanda sun cigaba da farautar sauran masu garkuwa da mutanen tun bayan lokacin, amma sai a safiyar ranar Laraba suka samu nasarar kama su bayan sun fito daga maboyarsu.

DUBA WANNAN: Asiya da Atika, kwararrun masu garkuwa da mutane sun shiga hannu a jihar Kebbi

"Mu na zargin cewa sun fito ne domin canja maboyarsu tunda basu san cewa jami'an mu na bibiye da su ba. Jami'an mu sun dira a kansu, kuma sun samu nasarar kama su baki daya. Mun samu bindigu guda biyu, karamin jirgin ruwa da wasu kayan tsafi a wurinsu," a cewar Oyeyemi.

Oyeyemi ya kara da cewa yayin da rundunar 'yan sanda ta debi masu laifin ranar Alhamis domin mayar da su hedikwatarsu ne sai abokansu suka kai wa 'yan sandan harin kwanton bauna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka kama da kuma daya daga cikin wadanda suka yi yunkurin kubutar da su.

Kazalika, ya bayyana cewa wasu daga cikin jami'an 'yan sandan da ke cikin tawagar raka masu garkuwar da mutanen sun samu raunuka yayin musayar wuta da aka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel