Daga cacar baki, jami’in hukumar kwastam ya dirka ma wani mutumi bindiga har lahira

Daga cacar baki, jami’in hukumar kwastam ya dirka ma wani mutumi bindiga har lahira

Hankula sun tashi a garin Ijebu Ode na jahar Ogun yayin da wani jami’in hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam ya dirka ma wani matafiyi bindiga wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa har lahira, akan ya hanashi cin hancin naira dubu biyar.

Majiyar Legit.ng ta bayyana wannan kisa ya faru ne a gaban jama’a kamar yadda wani bidiyo dake yawo a kafafen sadarwar zamani ya nuna, inda aka hangi wata mata tana ihu hannunta a kai sakamakon tashin hankalin da ta shiga ganin yadda kwastam din ya kashe mutumin.

KU KARANTA: Ku kawo min dauki, Gwamna na neman kassara ni – Inji Mataimakin Gwamnan jahar Kogi

Ita ma hukumar kwastam ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta musanta zargin kisan mutumin da gangan, inda tace tsautsayi ne kawai ya hau kan mamacin, sakamakon ba shi aka yi nufin harba da bindigar ba.

Kaakakin hukumar kwastam, Joseph Attah ne ya bada wannan uzuri, inda yace jami’an kwastam sun tare wata mota da suke zargin ta yi lodin kayan gwanjo zuwa Najeriya, amma sai fasinjojin cikin motar suka yi kokarin kwace makaman jami’an, a haka ne aka harba bindiga ta kashe mutumin.

“Fasinjojin wata motar Bus da ake zargi tana dauke da kayan gwanjo ne suka yi kokarin hana jami’an kwastam gudanar da aikinsu yadda ya kamata, hakan ya janyo rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar wani matashi mai suna Godwin, tare da jikkata wani jami’in kwastam Destiny Onebamho.

“Ba kamar yadda ake yayatawa ba, Godwin ba fasinja bane a cikin motar, matashi ne dake aikin debo ma jami’an kwastam ruwa a duk lokacin da suka dawo daga sintiri, bincikenmu ya nuna cewa a lokacin da fasinjojin motar suka yi kokarin kwace makaman kwastam ne wata bindiga ta tashi ta kashe Godwin.” Inji shi.

Daga karshe Attah yace hukumar ta nemi iyayen Godwin, sa’annan yace an dawo da tawagar jami’an na kwastam da rikicin ya shafa zuwa babban ofishin hukumar don kara gudanar da cikakken bincike game da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: