Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 2 a jihar Ogun
Hukumar kula da lafiyar manyan hanyoyi ta FRSC reshen Sango-Ota ta bayyana cewa, mutane biyu ne suka rasa rayukan su yayin da wasu da dama suka jikkata a sanadiyar aukuwar wani mummunan hatsari tsakanin Motoci 3 a babbar hanyar Ilo-Awela ta jihar Ogun.
Shugaban wannan reshe na hukumar, Mista Adekunle Oguntoyinbo, shine ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Ota.
Oguntoyinbo ya bayyana cewa, wannan hatsari ya afku ne da misalin karfe 9.45 na daren ranar Larabar da ta gabata.
Ya ci gaba da cewa, wannan hatsari ya afku ne tsakanin wasu motoci uku sakamakon tsala gudu da ya sabawa ka'ida tare da yiwa dokokin manyan hanyoyi karan tsaye.
Kamar yadda shafin jaridar Today Nigeria ta ruwaito Legit.ng ta fahimci cewa, motocin da samfurin kirar kamfanonin su sun hadar da; Mack mai lambar LND 615XP, Mazda mai lambar KSF 102XD da kuma tankar man fetur mai lambar APP 273XP.
Yake cewa, mutane biyu cikin 18 da hatsarin ya ritsa da su sun riga mu gidan gaskiya yayin da da dama daga cikin su suka jikkata.
KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta hada gwiwa da kamfanonin Fasahar zamani domin yakar labaran bogi
A halin yanzu an killace gawar wannan Mutane biyu a babban asibitin garin Ota yayin da sauran ke karbar magani da kulawa a asibitin Lead way kamar yadda Mista Oguntoyinbo ya bayyana.
Shugaban hukumar ya kuma shawarci masu ababen hawa akan sanya idanun lura da kuma tabbatar da lafiyar ababen su na hawa da hakan zai kiyaye afkuwar hadurra.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng