Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu manyan Limamai 5

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu manyan Limamai 5

Gungun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu manyan Limaman cocin ‘Redeemed Christian Church of God’ RCCG a jahar Ogun, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban cocin, Fasto Adeboye ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 2 ga watan Agusta, inda yace yan bindigan sun yi garkuwa da Fastocin ne a yayin da suke kan hanyar zuwa Legas don halartar babban taron cocin.

KU KARANTA: Majalisar Musulunci ta koli yi karin haske game da ganin watan Zulhijja

A cewar babban Faston, an kama fastocin ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta a kan babbar hanyar Ije-Ode, don haka ya yi kira ga mambobin cocin da su dage da addu’a don ganin Fastocin sun kubuta daga hannun yan bindigan.

Fasto Adeboye ya cigaba da cewa wannan ne karo na farko da irin wannan ke faruwa ga Fastocin cocinsu. “A matsayina na uba, ya kuke ganin zan ji ace an yi garkuwa da yayana guda 5?”

A wani labarin kuma, masu garkuwa da mutane a jahar Zamfara sun sako wani babban basarake, hakimin Kaba, Alhaji Buhari Ammani, tare da iyalansa, wanda suka sacesu tun kimanin watanni uku da suka gabata.

Yan bindiga sun yi awon gaba da Ammani da iyalansa ne a lokacin da suka kai wani hari a karamar hukumar Kaura Namoda na jahar Zamfara.

Babban hadimin gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, Abubakar Mohammed Dauran ne ya bayyana haka yayin da yake mika Ammani ga gwamnan, inda yace yan bindigan sun saki Ammani da iyalansa ne ba tare da wata sharadi ba, illa saboda matakin sulhu da gwamnatin jahar Zamfara ta dauka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng