An gano wani Otel da maza ke zuwa suyi zina da 'yammata su biyansu N500 a wata jihar Najeriya
- An gano wani otel da ake zuwa ayi zina da yara mata kanana a biya su naira dari biyar
- Otel din dai an gano shi a Shimawa ne, iyakar da ta raba jihar Legas da Ogun
- Yanzu haka dai an kama maza guda biyu da kuma mata guda goma sha hudu a cikin otel din
A ranar Larabar nan da ta gabata ne aka gano wani otel a Shimawa, iyakar da ta raba jihar Legas da Ogun, inda ake amfani da yara mata kanana ana zina da su ana biyansu kudi.
An kama maza guda biyu tare da yara mata guda goma sha hudu, wadanda suka ce sun zo daga jihohin, Akwa Ibom, Enugu, Kogi da kuma jihar Imo. Matan wadanda suka bayyana cewa kawayensu ne suka yaudaresu suka kawo su wannan waje daga kauyukan su, ana tilasta su su dinga baiwa maigidansu naira dubu daya a kowacce rana a matsayin kudin daki. Sannan kuma ana tilasta su kwanciya da maza akalla guda hudu a kowacce rana, inda ake biyansu naira dari biyar ko kuma dubu daya. Bayan kwanciya da ake yi da su a biyasu, an gano cewa mazan da suke da wajen suna kwanciya da su a duk lokacin da suka ga dama.
Wadanda aka kama a otel din sun hada da mai otel din Gbenga Olayinka, dan uwanshi Adekunle Oshineye, mata guda uku wadanda suka balaga da suka hada da Happiness Daniel, Favour Nkume da kuma Glory Ewelike.
Sai kuma yara mata kanana da aka gama a wajen da suka hada da Chisom Onyekwere, Chinonso Okoro, Stella Emmanuel, Gift Wada, Chidinma Emmanuel, Tracy Favour, Success Onu, Comfort Francis, Njoku Divine, Destiny Chibuike da kuma Amanda Chima.
KU KARANTA: Yarinyar da ta shekara ana nemanta ruwa a jallo, a karshe mahaifiyarta ta ganta a cikin fim din batsa
Da take magana da manema labarai akan yadda aka gano wannan waje, mataimakin sufurtanda na 'yan sandan jihar (DSP) Cordelia Nwawe ta ce shugabanta mataimakin shugaban hukumar 'yan sanda na kasa (AIG) Usman Mani shine ya samu labarin wannan waje ranar Talatar da ta gabata.
Mai otel din ya musanta cewa ya san wasu daga cikin 'yammatan, inda ya bayyana cewa wasu daga cikinsu sun karbi hayar dakunan ne da kansu na tsawon shekara biyu.
Shi kuma Oshineye cewa yayi an kama shi a dakin daya daga cikinsu wacce suke soyayya. Mutumin ya ce yana taimakawa kawun nashi ne da wasu ayyuka a otel din idan yaga cewa bashi da aiki sosai.
Haka ita kuma daya daga cikin 'yammatan da aka kama ta bayyana cewa ta zo wannan otel dinne shekara biyu da suka wuce bayan ta jima tana wannan harka ta karuwanci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng