Kwankwaso ko Obi: Atiku Ya Fadi Dan Takarar da Zai Iya Goya wa Baya a ADC
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam'iyyar ADC za ta yi amfani da tsarin fitar da dan takara ta hanyar maslaha ko kuma zabe kai tsaye
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma tabo batun janyewa wani daga cikin masu son takarar da ke neman tikitin jam'iyyar ADC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi maganar hakura da takara a zaben 2027.
Atiku ya bayyana cewa a shirye yake ya janye wa duk wani ɗan takara da aka amince da shi wanda zai fito daga cikin hadakar da aka gina a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC, ciki har da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

Source: Twitter
Atiku ya bayyana haka ne yayin wata hira a shirin Prime Time na tashar Arise News a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilun, 2026.
Atiku ya amsa tambayoyi kan zaben 2027
Atiku ya amsa tambayoyi kan haɗin kan gamayyar 'yan hadaka da kuma tsarin zaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa.
Yayin da aka tambaye shi ko zai janye domin samar da haɗin kai idan aka samu ɗan takarar da kowa ya amince da shi, Atiku ya ce babban abin da ya kamata a mayar da hankali kai shi ne ba da goyon baya, ba kawai janyewa ba.
“Ba batun janyewa ba ne, shin zan bayar da goyon baya ne? A cikin wannan hadaka, zaɓi na farko shi ne mu samar da maslaha kan mutum ɗaya. Idan hakan bai yiwu ba, sai mu tafi zaɓen fitar da gwani, kuma zan mara wa duk wanda ya yi nasara baya."
- Atiku Abubakar
Wane tsari ADC za ta yi amfani da shi?
Atiku ya jaddada cewa samar da maslaha kan mutum ɗaya shi ne babban zaɓi ga wannan hadaka ta jam'iyyu.
“Maslaha ita ce zaɓi na farko ga jam’iyyar, za mu yi ƙoƙarin cimma hakan. Idan ba mu samu ba, sai mu tafi zaɓe."
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Shin Atiku zai janye wa Peter Obi?
Lokacin da aka matsa masa da tambaya ta musamman kan ko zai janye wa Peter Obi idan aka ga ya fi shi farin jini, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya sake jaddada matsayarsa.
“Zan janyewa duk wanda ya yi nasara."
- Atiku Abubakar
Yayin da aka sake tambayarsa ko hakan ya haɗa da Peter Obi, Atiku ya amsa da cewa:
“Tabbas, idan yana takara, me zai hana.”
Atiku ya fadi lokacin daina takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana lokacin da zai daina neman mulkin Najeriya.
Atiku ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 shi ne zai zama fafatawarsa ta ƙarshe a fagen neman mulki.
Kalaman tsohon mataimakin shugaban kasar sun zo ne a daidai lokacin da ake ta mahawara kan makomar tsofaffin jiga-jigan siyasar ƙasar da kuma buƙatar ba matasa damar yin mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


